Yadda ake yin Bincike (search) da Google Search Engine (1)

0
549

Ba kawai za ka buɗe shafin google ba ne ka rubuta suna ko kuma wani abu da kake nema ba, shi ne kawai hanyar da za ka bi ka yi bincike. Google shi ne gidan da ya fi ko’ina shahara a internet kasancewar shi ɗaya daga cikin gidajen da suke ɗaukar ɗawainiyar fito da amsoshin abubuwan da mutane suke nema.

Google kamfani ne da ya shahara a bakin duk wanda yake amfani da internet, musamman wanda suke yawan bincike da neman bayanai, amma kuma google ba bincike kawai ake yi a cikinsuba, yana da ayyuka da dama da yake yi, wanda suka haɗa da kalanda, da akwatin ajiyar imel, ɗakin ajiyar takardu, youtube, video, document, translate, blogger, photos, shopping da dai makamantansu.

A wannan rubutu da zan yi, zan raba shi kashi uku, kashi na farko bincike mai sauƙi, wanda kusan kowa shi ya fi amfani da shi, sai dai kuma ana amfani da shi cikin kuskure, shi ne za mu yi don gyara a kai. Kashi na biyu kuwa za mu zurfafa binciken ne, ta wajen amfani da zurfafan hanyoyin yin bincike a shi google search engine, ta yadda yin amfani da wannan hanyar zai sauƙaƙa matuƙa da kuma fitar da sakamako mai inganci. Kashi na uku wanda kuma shi ne na ƙarshe shi kuma za mu yi bayanin hanyoyin da ake bi a binciken hotuna, video da kuma wurare a duniya baki ɗaya.

kamar yadda mafi yawa daga cikin mu muka sani, duk wanda yake da waya ko kuma yake da computer da yake son ya yi bincike shi ne ya shiga google. wanda kuma bai san yadda zai yi ba to, zai rubuta  www.google.com a wurin da ake rubuta adireshin shafukan internet wanda aka fi sani da Address Bar, da zarar ya rubuta zai duɗe mishi shafin farko.

A daidai lokacin da mutum ya rubuta abin da yake nema a google, misali ya rubuta Duniyar Computer  to bayan ya rubuta tambayar shi sannan ya latsa search to ya sani google zai shiga cikin taskar da yake ajiye bayanai na dukkanin shafukan da suke cikin internet a fito da kalmar Computer da kuma kalmar Duniyar sannan kuma zai yi ƙoƙarin ya fito da inda ya same su a haɗe. Shi ya sa idan mutum ya shiga internet domin ya yi bincike kuma ya shiga ɗakunan bincike irin su google da zarar ya rubuta tambaya sai kawai yaga sakamako akalla miliyan hamsin, wanda kai da kanka mai karatu ka sani cewar ba yadda za a yi tambaya ɗaya a ce tana da amsa sama da miliyan ɗaya ko ma a ce dukkansu daidai suke.

Shi ya sa yana da kyau masu karatu su sani cewar ba dukkanin sakamakon da ka yi binciken sa a google ba ne yake zama cikakken amsa ba. Dukkanin wasu kalmomi da ka rubuta cikin ɗan ramin da google suka bayar a rubuta zai fito maka da amsoshin iya adadin kalmin. Misali da mutum zai rubuta how can I write English to abin da google zai yi maka shi ne duk inda aka rubuta kalmar how a internet zai fito da ita. Haka kalmar can zai fito da dukkanin shafukan da aka rubuta wannan kalmar, haka zai ta fito da kowace kalma ɗaya bayan ɗaya, sai ka samu amsa sama da miliyan goma amma kuma da wuya ka sani amsa tare da wannan cikakkiyar jumla kamar yadda ka rubuta ta.

Da wannan dalili ne ya sa su kansu kamfanin google suka fito da wasu hanyoyi da za su sauƙaƙawa masu bincike a internet wajen samun gamsasshiyar amsa. Saboda haka, za mu ɗauki waɗannan hanyoyi ɗaya bayan ɗaya mu yi bayanai a kan su domin mu sauƙaƙa muku domin yin bincike a google.

BINCIKEN JUMLA

Binciken kalma a google kamar yadda na yi bayani a baya kan iya fitowa da sakamako mai yawa wanda kuma ba su da dangantaka da abin da ake nema. Amma kuma idan ya zo ta ɓangaren ka san me kake nema, to, akwai abubuwan da za ka kiyaye wajen binciken. Duk wanda ya san me yake nema kamar kana son ka nemi wata jumla a internet ko kuma wani shugaba ya yi wani jawabi kuma ka hadda ce yadda ya faɗi kalmar kuma kana son ka karanta sauran labarin to, google sun bayar da hanyoyin da za ka bi idan ka haɗa da kalmar da kake bincike zai bada amsarka daidai.

·               Quotation Marks (Baka biyu) “  ” duk wanda zai yi binciken wani abu da yake son gani to sai ya saka shi a cikin baka biyu. Misali “Duniyar Computer” ko “Hankali ke gani ba ido ba” saka waɗannan tambayoyi a cikin baka biyu zai dawo maka da amsar ka a duk shafukan internet ba tare da ya kakkatse zuwa kalmomin ba.

·               Phrase Connector: su ne hyphen ( – ) ko slashes ( / ) ko period ( . ) ko equal signs ( = ) da kuma apostrophes ( ! ) waɗannan alamomi su ake kira da phrase connector su ma kamar yadda aka yi amfani da baka domin samun ainihin amsa, su ma haka ake amfani da su misalin duniyar-computer  ko duniyar.computer  ko hankali=ke=gani=ba=ido=ba  da sharaɗin ka da ka bada sarari a tsa kanin kowace kalma.

AMFANI DA LAMBOBI:

Mutum na iya binciken abu a google ta hanyar amfani da lambobi wajen bincikensa. A misalin mutum yana neman wani abu wanda kuɗinshi bai wuce kaza ba, to zai iya amfani da wannan tsari wajen yin binciken. Phone $40..$90 idan ka rubuta haka to google zai fito maka da wayoyin hannu wanda kuɗinsu bai gaza dala arba’in ba kuma ba su wuce dala casa’in ba.

AMFANI DA LOKACI

Idan mutum zai binciki wani abu a internet kuma wannan abin ya ƙunshi lokaci, to, za ka iya yin amfani da abin da ake kira Date Range shi kuwa Date Range ana saka shi ne a wajen binciken abubuwan da aka san lokacin faruwarsu da kuma ana kokwanton daga lokaci kaza zuwa lokaci kaza ne abu kaza ya faru. Kodayake shi amfani da wannan hanyar binciken tana da sharuɗɗa wanda sai an kiyaye su kafin a samu amsar da ake nema.

Misali wanda yake son ya yi binciken abin da ya shafi wani littafi wanda bashi da haƙiƙanin lokacin da aka wallafa wannan littafi amma kuma ya san bai wuce daga shekarar 2000 ba zuwa 2003. To, da farko dole ya rubuta sunan littafin sannan ya rubuta shekarar da yake tunanin ita ce aka wallafa shi, sannan ya rubuta ƙarshen shekara. Harry Potter daterange:2004-01-13..2006-01-13

AMFANI DA KALMOMIN CIKI (METADATA)

Wannan shi kuma tsari ne da kamfanin google suke baiwa masu binciken asalin kalma da ta ta’allaƙa ga shafuka da suke da kalmomin ciki wato ‘metadata’. Su metadata a taƙaice waɗansu kalmomin da aka saka su a cikin shafukan internet domin sauƙaƙawa shi search engine sauƙin gano shafuka da abubuwan da shafukan suka ƙunsa. Misali duk lokacin da masu ilimin sanin yadda ake shirya shafukan internet “web designer” suka ƙirƙkiri shafi, to zai rubuta waɗansu kalmomi da suke da alaƙa da wannan labarin da ke cikin wannan shafin. Kamar mutum ya rubuta labari game da computer kuma ya yi magana a kan abin da ya shafi Microsof Office, to, a wurin da ake rubuta shi metadata sai ya rubuta Kalmar Micrsoft, Windows, Office, Computer da dai waɗansu ‘yan kalmomin da ya san mai bincike a internet zai iya rubutawa don neman sani.

Wannan shi ne dailin da ya sa idan mai bincike ya shiga google domin yin bincike idan ya rubuta wata kalma sai yaga wani shafi ya bube amma kuma idan ya duba sama da ka san shafin zai ga babu wannan kalmar a ciki. To ita wannan kalmar tana ɓoye ne a cikin kalmomin ciki “metadata”.

To, wanda yake son ya binciki wani shafi amma kuma yana son shi shafin da yake binciken ya kasance a cikinsa ya ƙunshi kalmar kaza, to zai iya yin amfani da tsarin metadata wajen yin binciken. Sannan wani Ƙarin haske ma zai kuma iya ƙididdige lokacin da aka saka wannan bayani desertherald inmeta:modified:2006-01-01..2006-12-31 shi ma kamar yadda muke gani mun yi amfani da kalmar da muke nema, sai muka saka inmata wanda shi yake wakiltar google search engine, sannan kuma sai ka saka kalmar modified wato lokacin da aka gyara ita waccan kalmar da kake nema, sannan ka saka kwanan wata.

Wurin yin amfani da kwanan wata a wurin yin bincike a google mu kiyaye da yadda ake tsara date ɗin, kwanan watan da za ka rubuta na farko dole ya fara da shekara sannan wata sannan rana kamar haka 2006-01-01.

TACE KALMOMI WAJEN BINCIKE

Wannan ɓangare kuwa shi za mu nuna mai karatun wasu ‘yan hanyoyi ne da zai bi wajen neman kalma da kuma wata kalmar da ke da dangantaka da kalmar farko, ko kuma yana son ya yi binciken kalma amma kuma baya son kalma kaza ta biyo baya, ko kuma yana son ya yi binciken kalma amma kuma ta zo da kalma kaza tare da ita, ko kuma ya binciki kalma kaza amma kuma idan ba a samu wancan kalmar ba, to wata kalmar ta zo.

KALMA1 OR KALMA2 (KALMAR FARKO KO KALMA TA BIYU)

Idan mutun na son ya yi binciken kalma sannan kuma idan wannan kalmar ba ta samu ba, to a nemo wata kalma sai ka rubuta a cikin ramin google search engine duniya or lahira  rubuta kalmar or a tsa kanin kalmomin guda biyu shi ke faɗa wa google cewar a nemo mini kalma kaza ko kuma kalma kaza.

KALMA1 -KALMA2 (KALMAR FARKO BAN DA KALMA TA BIYU)

Idan mutum yana son ya yi binciken kalma amma kuma baya son ya zama binciken ya haɗa da kalma kaza to zai rubuta a cikin ramin google search engine misalin wannan ɓangare kuwa shi za mu nuna mai karatun wasu ‘yan hanyoyi ne da zai bi wajen duniya -lahira. Yin ha kanka faɗa wa google cewar a yi maka binciken shafukan da aka samu kalmar duniya amma kuma kada a samu kalmar lahira a cikin shafin. Amma wurin rubuta wannan hanya mutum sai ya kiyaye kada ya raba alamar ragewa ( – ) da kalma ta biyu.

KALAM1+KALMA2 (KALMAR FARKO TARE DA KALMA TA BIYU)

Idan kuwa mutum na son ya yi binciken kalmomi guda biyu lokaci guda, misalin yana son kalmar duniya amma kuma ya kasance an sami kalmar lahira a tare ko kuma a cikin shafi guda, to sai ya rubuta kamar haka duniya+lahira wanda ya rubuta haka zai sami sakamakon shafin da aka samu kalmar duniya sannan kuma aka samu kalmar lahira a cikin shafin gaba ɗaya. Shima kamar yadda na sama yake kada ka raba alamar haɗawa ( + ) tare da kalmomin da kake bincike.

KALMA (‘YAN UWAN KALMA)

Idan mutum na son ya yi binciken kalma amma kuma yana son a nemo mishi kalmomin da suke da alaƙa da wannan kalmar, to a nan zai saka alamar ( ~ ) a jikin ita kalmar. Misalin idan kana son waɗansu kalmomi ne suke da alaƙa wajen ma’ana tare da kalmar education,  to sai ka rubuta kamar haka ɓeducation yin ha kan zai fito da dukkanin kalmomin da suke da alaƙa kalmar education wanda a turance ake kira da synonyms.

~ KALMA -KALMA (‘YAN UWAN KALMA TA FARKO AMMA BAN DA KALMA TA BIYU)

Shi kuwa wannan binciken ya yi kama da na samanshi, sai dai kuma banbanci tsa kaninsu shi ne wannan kana buƙatar a kawo maka kalmomin da suke da alaƙa da wannan kalmar amma kuma baka son wanda suke da alaƙa da kalma ta biyu. Misalin ɓexamination -assignment  waɗannan kalmomi ne guda biyu masu alaƙa da junansu ta wajen ma’ana, to amma kuma idan ka saka irin wannan tambayar za a baka amsa da dukkanin kalmomin da examination yake da shi tare da alaƙanta kansa da shi, da kuma kin fito da kalmomin da suke da alaƙa da assignment.

Waɗannan su ne a taƙaice abin da za mu iya baku waɗanda suke shafi yin bincike tare da google search engine, nan gaba kaɗan za mu kawo kashi na biyu, Zurfafa bincike ta wajen yin amfani da google search engine

Da fatar za a kasance tare da mu a darasi na gaba. Ga neman ƙarin bayani ko tambaya zai iya aiko da ita kai tsaye zuwa ga info@duniyarcomputer.com.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here