Shin Ana Iya Leƙen Asirin Mutum Ta Waya Kuwa?

Amsa itace ‘e’ ana iyawa, domin mafi yawancin mutane da ke amfani da manyan wayoyi (smartphone) irin su Android, iPhone, iPad da mkamantansu tamkar kusan tsirara suke. Akwai mutane da kan iya ganin sirrin ka ta cikin wayar taka daga nesa. Babban abu ma shi ne akwai waɗansu Apps da idan ka sake ka sa su a wayar ka za su fara aiki a boye (background) kai tsaye har ma da amsa kuwar ɗin wayar ka (microphone) ta ɗaukar maganganun ka tana aika wa da su. Ƙarami daga cikin irin waɗannan Apps ɗin shi ne stealthGenie (spyware) yakan zama abin da ake cewa Trojan kuma yana iya aiki da iOS dinka, kai hasali ma yakan yi amfani a Android da Blackberry ya aika taswirar (geolocate) ɗinka ya kuma saurari maganganunka, saƙonnin rubutu (text messages) da hotunan ka ya aika da su kowane lokaci.
Wani kamfanin da ya ke yin irin waɗannan Apps sun taɓa yin alfaharin cewar suna da mutane (customers) sama da dubu ɗari (100,000) duk da dai hukumar tsaro a Amurka ta cafke shi shugaban wannan kamfanin.
Za mu iya tunawa da maganganu da ɗan leƙen asirin nan na Amurka wato Edward Snowden da ya yi na cewa gwamnatin Amurka tana leƙen asirin cikin wayoyi, saƙonnin e-mail da sauransu al’amuran intanet na mutane da yawa a cikin duniya. Wannan magana ta tsohon jami’in CIA ta tabbatar mana cewar lallai NSA na amfani da hanyoyi daban-daban wajen neman sirrin mutane.
Akwai wani Apps da ake kira da suna Angry birds shi ma yana ɗaya daga cikin Apps da ake amfani da shi wajen leken asirin.
Saboda haka nake ganin ma cewar ka kiyaye zuwa banɗaki da wayar (smartphone) domin tana iya maka tonan silili.
Masu bincike a jami’ar Stanford sun gwada wani Apps (Gyrophone) domin tabbatar da irin wannan zargin kuma sun ta gano cewar lallai amsa kuwar waya (microphone) kan iya aika sautinka, kai har ma da gano wanda ke yin magana. Wannan Apps na da ƙarfin tafiya a iska na 80 – 250 Hz a kan iska.
Sun gano da tabbatar wa duniya cewar amfani da wannan Apps (Gyrophone) za a iya gano mai magana dama mai amsa maganar. Sun gwada a kan wayar Android ya yi aiki yanzu ma har sun fara gwadawa a kan iPhone.
Wasu jami’oi ma kamar Citizen lab a jami’ar Toronto sun yi wannan gwajin da gano masu leƙen asiri ta irin wannan hanyar a ƙasar Italiya. An tabbatar cewar masu leƙen asirin suna amfani da GPS tracker na amsa kuwarka da zaran ka hau yanar gizo (internet) ta Wi-fi.
Binciken ya nuna cewar akwai manyan kwamfutocin da ake amfani da su wurin leƙa sirrin mutane (computer servers) sama da guda 350 a ƙasashen duniya guda 40 da ake amfani da su. Abin tambaya a nan shi ne, gwamnatocin sun san da haka kuwa? Idan ko sun sani ke nan su ma suna leƙen asirin wayar mutanensu.
Saboda haka ka lura domin wayar ka ta smartphone da kake tunƙaho da ita kake maƙale da ita kullum da guje wa kaɗaici mai tona ma ka asiri ce. Saboda haka abin sai addu’a.

Get in Touch

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Get in Touch

19,723FansLike
2,188FollowersFollow
8,322SubscribersSubscribe

Latest Posts

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin...

Yadda Wayar Selula take yin aiki

Yawancin mu a wannan lokaci wayar hannu ta zaka bangaren rayuwar mu, amma kuma nasan daga cikin tambayar da muke bukatar amsarta shine wai...