Protocol Me Wannan KALMA take nufi?

0
553

Protocol

Wannan kalma ta Protocol tana da matukar muhimmanci ta fannin sadarwa (Communication Technology) ta bangaren da ya shafi Computer. Ita Kalmar Protocol ararriyar kalma ce daga Girkawa wanda take nufin fallen takarda guda, wanda ya ƙunshi dukkan bayanin da ke cikin littafin wannan falle.

Amma idan muka danganta wannan kalma a ilimi na Computer ko Information Technology, yana da fage na musamman a bangaren cikakkiyar hanyar sadarwa ta Communication. Idan muka dauki ita wannan kalma ta Protocol zamu ga cewar ana samun ta kusan a kowane fage na hanyar isar da sako ko kuma tabbatar da ingantacciyar hanyar aiko da sako daga na’ura zuwa wata na’ura. Kamar TCP/IP wanda ke nufin Transimission Control Protocol ka ga an sami kalmar a nan, Haka IP, shi ma Internet Protocol ita ma ga kalmar a ciki, haka HTTP wato Hyper-Text Transfer Protocol da dai makamantansu.

A misali, ana samun kalmar Protocol a cikin kowace hanyar sadarwa ta computer kamar yadda muka gani a wadannan kalmomi na baya, ko dai a sami tsarin Protocol a device (Dukkan wani abu da yake amfani da wutar lantarki ko kuma batir shi ake cewa device) ko kuma a application.

Idan ka hada computer da Internet lokacin da ka kunna Internet Browser domin fara amfani da wani shafi daga internet to su TCP/IP su suke da alhakin kai wa da karbar dukkanin abin da mutum ke gani ko ke aika wa.

TCP na nufi Transmission Control Protocol, wato Protocol ne wanda yake da alhakin watsa dukkanin bayanai da ita internet take da shi, wanda shi TCP shi ne kuma yake iya hada Kwamfutarka da  zamu iya cewa dukkanin wani kulla alaka a tsakanin na’urori guda biyu, misali waya da waye, computer da computer ko kuma waya da computer to suna bukatar tsari guda da zai ba su damar kulla wannan alaka, to dukkan wani tsari da zai daidaita tsakanin su shi ne ake cewa Protocol.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here