PORT – Mahada a Computer

Port

Port wuri ne da yake baka damar hada kayan computer da suke wajen system unit kamar printer da scanner da makamantansu. To shi ramin da ake hada wannan wayar da ta fito daga jikin shi wancan hardware zuwa jikin system unit shi ake kira da port, kodayake wajen da ake hada wadannan hardware sun kasu kashi biyu.
1. Serial Port
2. Parallel Port

Serial Port

Shi serial port daya ne daga cikin port da ake hada kayan computer da system unit amma ana amfani da serial port a irin kayan computer wadanda ba sa bukatar sauri wajen isar da sako ko kuma fitar da sako. Domin serial port yana aika wa da sakon data daya ne a kowanne dakika daya. Kayayyakin da suke zuwa da mahada irin ta serial port su ne mouse da keyboard da kuma modem. Sannan serial port yana amfani da RS-232 ko RS422 wanda shi ke tabbatar da yawan hakora da yake da shi, kusan serial port da ake amfani da su guda biyu male 25-pin (mai hakora 25) da kuma male 9-pin (mai hakora 9)
Ba kamar serial port ba, shi parallel port mahada ce da za ta iya turo da sakon data fiye da bit daya a dakika daya, dalilin kirkiran paralle port shi ne domin magance matsala da za a iya samu a wajen kayan hardware da suke bukatar sauri wajen isar da sako.

Parallel Port

Mafi yawancin Printer da ake da su suna amfani da mahadar Parallel port ne, wanda ya ke da zubin hakora 25 (famale 25-pin). Shi parallel port yana iya karBa ko aiko da sako da ya kai bit 8 a kowane dakika ta layi guda takwas a lokaci guda. Wani lokaci ana kiran Parallel Port da Centronics bayan da kamfanin da suka fara kirkiran shi su ka fitar da tsari da kuma dalilai da yasa computer za ta samu alaka tsakaninta da printer. Kamar Serial Port su ma Parallel sun kasu kashi biyu, akwai Parallel port da ake kira da EPP (Enhanced Parallel Port) da kuma ECP (Extended Capabilities Port) suna amfani da mahada irin ta Centronics port, amma sun fi centronics port saurin aika wa da data har sau goma.

Duniyar Computer
Salisu Hassan wanda aka fi sani da Salisu Webmaster shine shugaban wannan Muhajja ta Duniyar Computer kuma shugaban kamfanin Duniyar Computer, yana da kwarewa a fannoni da dama na Computer, ya kirkiri shafuka da manhajoji na computer da waya masu yawa, yana da kwarewa a fanni addinin Musulunci, yana jin Turanci da Hausa da Larabci. Magidanci ne kuma yana zaune a garin Kaduna a halin yanzu.

Get in Touch

Leave a Reply to abdul zango Cancel reply

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Get in Touch

19,710FansLike
2,180FollowersFollow
8,322SubscribersSubscribe

Latest Posts

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin...

Yadda Wayar Selula take yin aiki

Yawancin mu a wannan lokaci wayar hannu ta zaka bangaren rayuwar mu, amma kuma nasan daga cikin tambayar da muke bukatar amsarta shine wai...