MU CANZA SALON TSARO A MASALLATAI

0
2153

Kasancewar abubuwa na tashin hankali da suka faru a garin Adamawa da Kano in da aka rasa rayukan mutane da dama da kuma rahoton da na karanta a babban shafin JIBWIS Nigeria na cewar an kama wasu da kayan agaji da ake zargin ‘yan Boko Haram ne, naga ya dace nima in yi amfani da wannan kafar domin kira ga dukkan Al’ummar Musulmi da cewar a kara tsaurara matakai a dukkanin Masallatayyar mu.

Muna kira ga dukkanin shuwagabannin Agaji na kowane fanni, musamman JIBWIS, FITYANU, HIZBAH, JNI da su tsaurara matakai a dukkanin wurin da suke tura ‘yan agajinsu, sannan kuma su sanya wadansu alamomin ga dukkanin wadanda aka ce sune ke da duti a kowace rana. Su kuma hana duk wanda bashi da duti sanya uniform ko kuma yin aikin da ba a sa shi ba.

Kada ka raina kokarin makashinka domin zai iya amfani da kowace irin dabara domin ganin ya cutar da kai. A sanya shingaye na bincike nesa da masallaci, a kuma fara tsare wurin ibadu tun da safe.

Su kuma jama’a don girman Allah ku kara ba dukkanin jami’ai goyon baya, domin suna siyar da ransu domin su ga ran ka da na sauran al’umma ya kubuta. Duk irin abin da ‘yan agaji suka umarci jama’a da su yi mu taimaka mu yi.

Wannan musiba da take sake salo dole kowa shima ya canza salo.

Matakai da jama’a za su dauka bayan a masallatai ya kasance har da kasuwanni, sannan kuma a guji yin taron da zai tara daruruwan al’umma a wuri guda. Haka a kauracewa duk wani abu da ba a gane mishi ba.

Wannan zai kara taimakawa wurin tsare dukiyar jama’a a ciki har da taka da ta dan uwanka, da abokanka, da surukanka, da malamanka, da iyayen ka baki daya.

Allah Shi ne masanin abin da ke faruwa, kuma shi ya baiwa kansa masaniya game da irin kokari da hukumomin suke yi. Amma lallai muma sai mun tashi tsaye wurin ganin mun kau da duk wani irin abu da bai kamata ba.

Allah Ya saukaka mana al’amuranmu.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here