Mene ne wajibi ga me sabuwar computer?

2
672

Salam, Na sayi sabuwar Laptop computer. Menene suka zama wajibi ga wannan sabuwar system dina dan samun biyan bukata a gareni? Na gode. 21 August at 04:35

Duniyar Computer Malam Mustapha Adam da farko dai ya kamata ka sani cewar ita computer wani kayan aiki ne da zai iya samar maka da sauki a kowa ne bangare kake bukatar neman sauki. Sannan kuma ka danganta ita wannan computer take da sana’arka ko kuma ince aikin ka wato irin aikin da kake yi shine irin program da yaka mata ka saka. Amma idan kuma kana son kayi amfani da ita wajen koyon yadda zaka rinka sarrafata to Application na farko da ya kamata ace shine a computerka shine Microsoft Office Suite. Shi wannan program zaka iya yin abubuwa da dan dama, kamar fahimtar yadda zaka rinka sarrafa rubutu yin lissafi ajiya da kididdiga da dai makamantansu: 21 August at 08:31

2 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here