Alamomin da ake iya gane ko Kwamfutarka ta kamu da Virus ko kuma ba ta kamu ba.

 • Kwamfutar tana tafiya a hankali ba kamar yadda ta saba ba.
 • Makalewa wani lokaci
 • Kwamfutar ta rika kashe kanta tana kunna kanta wani lokaci.
 • Wani application ya rika nuna maka baya aiki kamar yadda ya kamata.
 • Hard Disk ko makamantansu idan ka saka su su nuna maka cewar baka saka suba, ko kuma ba za ka iya aiki da su ba.
 • Ya zamanta ba zaka iya printing ba yadda ya kamata.
 • Sakwannin matsaloli da b aka san da su ba.
 • Lalacewar menu ko rikicewar su ko kuma dialog boxes.
 • Wani lokaci sai ka ga hakkin mallakar document (extention) ya maimaitu sau biyu ko fiye ga duk wani sako da ka bude shi kamar ka ga .jpg ko .vbs, ko .gif ko .exe sun bayyana har sau biyu
 • Kawai ka ga anti-virus software din ka ya daina aiki haka kawai ba tare da wani dalili b aba kuma kai katsayar da shi ba, ko kuma shi anti-virus software din ya ki tashi kwata-kwata.
 • Ko kuma ka ga ka kasa saka anti-virus software a cikin computer, ko kuma ya ki fita daga cikin computer.
 • Bakin icons (maballai) ba da babu su a cikin Kwamfutar.
 • Bakon waka ko kuma sauti ya fara fitowa daga speaker ta computer wanda kai ba kai bane ka kunna wanan sauti, kuma inda ka kashe computer wani lokaci sai ta sake saka wannan sautin.
 • Haka Kwamfutar ta ki tashi, gashi kuma kai baka yi wani ayyanannen canji ba, baka saka wani sabon program bah aka kuma baka cire wani program ba..
 • Modem da kake browsing da shi ya rika yin wadansu aiki da ba kai ne ka saka shi yayi ba, ko kuma ya rika harba wutar aiki da sauri fiye da yadda ka san cewar haka yake yi. Wannan yana faruwa ne a lokacin da ka saka software da aka gurbatasu kai kuma baka san an gurbata su ba (pirate software).
 • Windows din ka ba  ya ki tashi sabo da wani hamimmin file ya bace, wani lokaci ma sai an lissafa maka files din da suka bace.
 • Wani lokacin idan an tsahe ta zata tashi kamar yadda aka sa rai, amma kafin ta kai desktop sai ta makale ko kuma kafin ta nuna icon na desktop kima kafin taskbar ya bayyana.

Get in Touch

 1. Ina da matsala daya, wato :: Wani lokaci sai ka ga hakkin mallakar document (extention) ya maimaitu sau biyu ko fiye ga duk wani sako da ka bude shi kamar ka ga .jpg ko .vbs, ko .gif ko .exe sun bayyana har sau biyu: dan Allah me ya kamata inyi.

Leave a Reply to samaila a.ubale Cancel reply

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Get in Touch

19,714FansLike
2,184FollowersFollow
8,322SubscribersSubscribe

Latest Posts

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin...

Yadda Wayar Selula take yin aiki

Yawancin mu a wannan lokaci wayar hannu ta zaka bangaren rayuwar mu, amma kuma nasan daga cikin tambayar da muke bukatar amsarta shine wai...