HANYOYIN SANIN CIKI DA WAJEN COMPUTER

3
900

Kadan daga cikin abubuwan da ake samu a bayan na’ura mai Kwakwalwa, takaitaccen bayanin abubuwan da suke a bayan computer, da amfanin su da kuma yadda ake jona su.

Power Switch

Wuri ne da ake sarrafa matatar wutar da take shige cikin Computer, yana da alamar kunnawa da kuma kashewa, idan ka latsa wajen da ya nuna alamar sa’adda yana nufin ka bada damar wuta ta shiga cikin matatar wuta, idan kuma ka mayar wajen da ya nuna a alamar sufuli, to wutar lantarki ba za ta sami damar shiga cikin matatar ba.

Power Code

Wuri ne da aka saka wayar da za ta aika da wutar lantarki daga jikin bango zuwa matatar wuta (Power Supply Unit)

Current Controller

Ana amfani da wannan wuri domin sarrafa yanayin karfin wutar da ake son ta shigo cikin power supply, sau tari za ka samu an daidaita tsarin karfin wutar 230v amma idan kana irin kasar da wutar su bata kai haka ba za ka canza shi zuwa 110v.

Power Supply

(Mai Sarrafa Wuta) wuri ne da ake sa wa na’ura mai kwakwalwa wutar lantarki, shi ne abin da yake baiwa dukkanin abubuwan da ke cikin uwar allo wuta (Motherboard), shike iya tace wutar da za’a baiwa dukkanin sauran kayan karafan da ke bukatar wutar zuwa wutar da ba za ta lalatasu be, Kamar, CD/DVD Rom, Floppy Disk, Hard Disk da dai makamantansu. Kuma shi Power Supply yana da hakora uku wanda ake kira da three-pin connector. Haka wani lokaci a jikin shi Power Supply a kan samu abin da ake kunnawa da kashewa (on/off), wanda yake taimaka wa wajen kunnawa da kashe na’urar.

Keyboard da Mouse

Wadannan wurere ne da ake jona keyboard da mouse, babu wani abu da ake jonawa ta wurin sai su, kuma su ma ana’urori na zamani an musanya su da USB.

Parallel Port

ga al’ada ana amfani da shi wajen jona Printer, do yake shi parallel port bashi da saurin tafiya, ma’ana idan aka jona printer ta parallel port to sai an kashe na’urar an kunnata sannan ta fahimci cewar an sama ta printer, amma yanzu an musanya shi da usb port domin saurin hadawa da na’ura

Monitor Socket (VGA)

wannan shi ne ake hada monitor da CPU domin ganin abin da yake faruwa a cikin na’urar. Ana iya samun wurin da za ka jona TV wanda ake kira da S-Video.

Ethernet Port

ETHERNET PORT:- Ana kiran shi da Network port, wannan wuri zai baka dama da hadana’urarka da sauran naurori ta hanyar internet ko network ko ya baka dammar hadana’urarka da broadband modem ko router.

USB Ports

A wannan zamani mafiya yawan kayan na’ura mai kwakwalwa ana hadasu da na’urar ta USB wanda cikakken ma’anar shi tana nufin (Universal Serial Bus). Ana jona mafiya yawan kayan na’ura ta wannan wuri, kuma masana sun ce a jikin USB guda daya, za a iya jona kayan computer sama da 75, kamar su Printer da kamar su Scanner. Na’urorin computer na zamani suna da USB 2.0 wadanda suna da karfi wajen tafiyar da kowane irin kayan na’ura da sauri.

Firewire Ports

Wannan shi ma wata mahada ce mai tsananin sauri, firewire yana taimaka wa wajen cire abida ke cikin wadansu na’urori wadanda ba computer ba ne, kamar kyamara ta majigi, ko kamara ta daukar hoto mara fim, da kuma abin sauraron sauti na Mp3 (player). Idan na’urarka bata da firewire a jikinta za ka iya sayen devices masu USB a jikin su, amma dole ya zama saurin USP da ke jikin devices ya zama saurin shi ya kai karfin tafiya ko saurin 2.0.

Sound Card

Ka yi amfani da kananan ramuka nan wajen jona speakers da kuma microphone. Amma idan kai ma’abocin son amo ne (sound) ko kana amfani da kayan amo manya, tun daga manyan speakers, kayan kide-kide (instrumental), to kana bukatar karin sound card ana’urar ka, domin Audio connectors ba su da karfin da za su dauki irin wadannan kayan amo.

Modem Port

Wannan ita ma mahada ce ta na’ura wanda mutum kan iya jona wayar tangaraho a jikin na’ura. Idan mutum yana son samun mahada ta internet da abin da ake cewa dial-up internet wanda yake amfani ta wayar tangaraho, to ta wannan ramin ake hadawa.

3 COMMENTS

  1. Muna jin dadin kasancewa tare da Duniyar computer a koda yaushe saboda ililimukanda muke samu

Leave a Reply to muhammad buhari Cancel reply

Please enter your comment!
Please enter your name here