GetJar

GetJar

 Daya ne daga cikin dakunan ajiya a Internet wadanda suka yi fice matuka wajen ajiye application na wayar hannu. Daga lokacin da suke bude wannan daki zuwa yanzu sama da mutane miliyan biyu suka saukar da application daga wurinsu. Ko da yake kamfanin ba wai Jar Application kadai yake ba yarwa ba, yana ajiye da Applicatin na wayar hannu fiye da dubu dari da hamsin wanda kusan mafi yawan wayoyin suke amfani da shi, wadanda suka hada da wayoyin masu tsarin Android da kuma Blackberry da kuma JAVA, da kuma Symbian da kuma Mobile Web. Ana samun kowane irin application na waya a wannan dakin ajiya sannan kuma sun tsaftace kayan su kasancewar duk abinda ka shiga ka dauka a cikin shafukansu zaka samu babu wani cutarwa ko kuma virus tare da shi. Haka kuma shi wannan website idan ka shigeshi da wayar ka zai gano wane irin wayace kake amfani da ita sannna ya tattaro dukkanin application da yasan zasu yi aiki da wayarka ya kawo su kusa da kai. Duk da cewar kusan kayan da ake samu a wannan shafi kyautane amma zai iya yuwuwa a samu wasu ba na kyauta ba. Kadan da ga ciki Applications da ake samu a wannan gida na internet sun hada da Dictionary na karatun a yaruka daban-daban, ka kowace irin browser, da kuma littatafai na koyan yaruka, da dai makamantansu. Ba banza ba a shekaran 2010, GetJar aka rada musu suna Technology Pioneer Award Winner . GetJar tana da helkwata a Silicon Valley mai ofishi a Ingila da kuma Lithuania. Domin neman karin bayani zaka iya shiga website na su a www.getjar.com

Kididdigar GetJar:

  • Abubuwan da aka saukar 2,087,181,833+
  • Yawan Games da Application da suke ciki 259,299
  • Yawan mutane masu kirkiran Application da suka yi rigista 367,124
  • Yawan kawunan waya da suke iya aiki da su 2,567.

Get in Touch

  1. Assalamu alaikum da fatan duk kuna lafiya.wallahi bazan iya nuna matukar farin cikina da wannan mujallah ba.sai dai kawai ince daku :ya rabbi allah ya taimakeku ya baku karin ilimi da lafiya da basira.kuma ya baku juriya.mun gode bisa kyaukyawar niyyarku.mai kaunarku mahammed saminu tasawa jahar maradi niger.

  2. Comment: salam barka da warhaka don Allah ina da tambaya menene asalin tashar TV ta taba ka lashe? kuma wanne dalili ne yasa aka bude tashar?

Leave a Reply to Nura Cancel reply

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Get in Touch

19,697FansLike
2,179FollowersFollow
8,322SubscribersSubscribe

Latest Posts

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin...

Yadda Wayar Selula take yin aiki

Yawancin mu a wannan lokaci wayar hannu ta zaka bangaren rayuwar mu, amma kuma nasan daga cikin tambayar da muke bukatar amsarta shine wai...