Ramadan Web Design

  4
  4055

  Wannan darasi ne da muka gabatar a watan Ramadan domin dalibai wadanda suke son su koyi yadda ake kirkiran shafi na Intanet.

  A wannan kwas mutum zai iya sanin dukkan wadansu surkulle da ake yin amfani da su domin kirkrian shafukan Intanet.

  Duk da karatun anyi shi ne a cikin aji tare da dalibai, amma Malamin yayi kokari wurin ganin ya yi bayanai masu gamsarwa game da hanyoyi da kuma ilimi da mutum zai yi amfani da su domin sanin yadda ake kirkirar shafuka a Intanet.

  Kasancewar darasi ne a kwanaki 12 kuma an tattara kusan fannoni da dama da ake bukatar saninsu wurin gina shafuka a Intanet tun daga abin da ya shafi darasi a matakin farko na sanin hanyoyin HTML da CSS da amfani da Notepad wurin gina shafi, haka amyi amfani da Abode Dreamweaver domin karasa karatun.

  Haka zalika, an koyar da yadda ake amfani da manhaja ta WordPress domin sanin yadda gidajen jaridu da mujallu suke amfani da wannan tsarin wurin kirkirar shafukan da suke yada labarai.

  Za ayi hakuri da surutu da tambayoyin dalibai kasancewar darussan dukansu anyi su a gadan dalibai kuma ambasu damar suyi tambayoyi kamar yadda aka sani a alada ta makaranta.

   

  Next articleKOYI WEB DESIGN A AWA 24
  Salisu Hassan wanda aka fi sani da Salisu Webmaster shine shugaban wannan Muhajja ta Duniyar Computer kuma shugaban kamfanin Duniyar Computer, yana da kwarewa a fannoni da dama na Computer, ya kirkiri shafuka da manhajoji na computer da waya masu yawa, yana da kwarewa a fanni addinin Musulunci, yana jin Turanci da Hausa da Larabci. Magidanci ne kuma yana zaune a garin Kaduna a halin yanzu.