Computer Software Gamsasshen bayani akansu

Computer Software, Software ko kuma kace Compter Program na nufin abu guda daya, amma abinda suke nufi shine, wadansu tarin rubuce-rubuce ne da ake dunkulesu wuri guda da ake son su sarrafa Hardware ko kuma su fadawa computer ga abinda zata yi.

Kamar misali irin wadannan umarni na computer sune suke baka damar idan ka danna maballin da ke jikin keyboard ita na’urar ta fahimce irin maballin da aka danna, ba domin Software da aka tsara zai rika fassara abinda keyboard ke yi ba da ya zama bashi da amfani. Haka kuma ta fannin program har ila yau, idan kayi amfani da keyboard ka yi rubutu su wadannan umarni sune suke da alhakin su ajiye shi cikin memory na computer wani software ya sarrafa shi.

Shi kuma wani software zai dauko wannan data da aka ajiye a cikin memory domin ya mayar da ita ta koma information. Wani umarnin shi kuma yana baka damar yin lissafi ne ka hada wancan data da wancan ya baka amsa. Haka wani umarnin yana baka damar ka fitar da sakamakon aikin ka zuwa takarda ko kuma ka ganshi a jikin monitor. Kusan kamar yadda muka fada babu yadda za’ayi Hardware yayi aiki ba tare da software da yake sarrafashi ba. Kafin computer ta yi wani aiki ko kuma ta gabatar da wani umarni shi umarnin dole a ajiye shi a cikin memorin nata. Ko da yake a zahiri wadannan ajiyayyun umarnin suna fitowa ne daga babbar kwakwalwar computer zuwa memori duk sa’adda aka kunna ita wannan na’ura.

Idan ka siya Program na Computer yana iya zuwa ne a cikin CD ko DVD, sai ka saka shi a cikin na’urar ka ajiye shi, domin idan har kana bukatar wannan Software da ka siya yayi aiki sai ka ajiye shi a cikin na’urar wato (Installation). Shi yasa wani lokaci ana yin Installing proram kai tsaye a cikin memory daga jikin Floppy ko CD ko DVD ko Flash Drive wanda yin haka ba sai ka sake ajiye shi a cikin Hard Drive ba. Saboda haka software shine ginshikin aikin computer, idan kana da ingantaccciyar software to na’urar ka zata zamar maka babban kayan aiki wanda zaka sami dimbin amfanin ta, kuma ka samu sauki wajen saukaka aikin ka. Saboda haka software ta kasu kashi biyu System Software da Application Software.

Get in Touch

Leave a Reply to Yahaya hoga Cancel reply

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Get in Touch

19,710FansLike
2,180FollowersFollow
8,322SubscribersSubscribe

Latest Posts

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin...

Yadda Wayar Selula take yin aiki

Yawancin mu a wannan lokaci wayar hannu ta zaka bangaren rayuwar mu, amma kuma nasan daga cikin tambayar da muke bukatar amsarta shine wai...