CI GABAN DA WAYA TA SAMAR A HANYOYIN SADARWA

0
501

Rubutawa: Salaha Wada Wali

Ba a taba samun sauki wajen harkar sadarwa ba kamar yadda muka sami hanyoyin sadarwa iri-iri a wannan karnin. Hakika idan muka dubi bangaren ci gaba da aka samu ta harkar waya a wajen sadarwa za mu fahimci cewa lallai sadarwar waya ta taimaka wajen saukaka aikace-aikace da kuma aika wa da sakonni da makamantansu.

Ka dubi sauki da aka samu a wajen magana a ko’ina tare da Wayar-Tafi-Da-Gidanka wanda a da kamar ‘yan shekarun baya ko ita kanta waya ana amfani da tangaraho ne wacce sai dai ka je jikin bango ko kuma wani sako da aka ajiyeta ka je ka amsa wayar. Amma idan muka duba Wayar-Tafi-Da-Gidanka za ka ga cewa abin ya zamanto mafi sauki matuka yadda a da sai dai ka sami layi guda tal a gida guda ko da kuwa akwai kowanne tangaraho da yawa. Amma a wannan lokaci za ka samu cewar a gida guda sai a sami kawunan wayoyi da layi ka daban-daban wanda idan aka sami gida guda tare da samari kamar goma sai ka samu dukkansu suna da waya kusan kowanne da hanyar wayar da yake amfani da shi fiye da daya.

Ana amfani da Wayar-Tafi-Da-Gidanka  wurin ajiye ajiye kama daga ajiye hotuna, hoto mai motsi, sauti kamar karatuttuka, wakoki da dai makamantansu.

Idan kuma muka duba ci gaba da wayar Salula ko kuma Wayar-Tafi-Da-Gidanka ta kawo ta fannin saukaka sadarwa zamu iya danganta shi da nasara mai yawa, kama daga yadda muke so mu rinka magana da abokan huldar mu, ko kuma dangi, zamu ga cewa lallai waya ta saukaka, idan kuma ta zo bangaran sakon karamin wasika shi ne zamu ga yadda waya ta bada sauki wajen aika wa da rubutaccen sako (SMS) sa’annan kuma ga sako wanda ya fi karamin rubutu wanda ake kira da MMS wato (multimedia message)wanda za ka sami cewar za ka iya daukar sauti, ko karatu ko waka, ka aika da ita zuwa ga abokin hulda kamar yadda kake aika wa da karamin sako. Kamar yadda kake iya aika wa da sauti (Audio) haka za ka iya aika wa da hotuna da kuma hoto mai motsi (Video), wanda a wancan lokacin na baya idan ka ce hakan zai faru ta harkar sadarwa ko ni mai rubutu  zan karyataka.

Ba ta wannan kadai ba ne hanyar sadarwa ta kawo ci gaba ta amfani da waya, ba idan muka dubi yadda ake amfani da wadansu kayayyaki wajen sarrafa sako ko kuma ita kanta wayar sai muga abin kamar sihiri. Mu dauki yadda ake amfani da Bluetooth na zamani wajen amsa waya da kuma yin wadansu al’amura, kama da karbar sakon waya, wanda suka shafi rubutu, ko sauti ko kuma Video da dai makamantansu dukkan su muna iya amfani da Bluetooth wajen sarrafawa. Haka idan kana amfani da Bluetooth na zamani sai ka ga cewar za ka iya yin zance na rubutu na kai tsaye (chat) da mutum ba  tare da hannunka ya taba  jikin handset din ka ba. Ga shi kuma babu wata harkar joni da waya daga wani abu zuwa jikin wani abu.

Har ila yau ana amfani da Wayar-Tafi-Da-Gidanka wajen shiga Internet wanda ya zamanto shi wani fage ne na musamman a harkar sadarwa. Bayan  iya shiga intanet ana kuma iya bude shafukan intanet din, haka kuma idan kana amfani da waya wacce take da WAF ko da karama ce a jikinta za ta iya zama wani kundi da za ka iya amfani da ita ta hada ka  da intanet din, wato za ka iya mayar da ita a matsayin  modem (Abin sadarwa) wanda za ka iya hada ta da computer ta Desktop ko kuma Laptop wajen shiga Internet. saboda haka Wayar-Tafi-Da-Gidanka ta taimaka maka wajen karfin sadarwa.

Wani abu da na ci gaba kuma , shi ne yadda ake amfani da waya ka kira mutum kana ganin shi yana ganin ka (video-call) wanda za ka iya yin magana da mutum kana ganin shi yana ganinka kamar kuna tare a wuri guda.

Ana amfani da Wayar-Tafi-Da-Gidanka wajen harkar tsaro, ko dai  gida, ko kuma abin hawa. Misali ta bangaren abin hawa za ka iya hada wayarka tare da mota ta wajen lura da yanayin da motarka take ciki a inda ka ajiyeta. Misali za ka iya hada kai da daya daga cikin kamfanonin sadarwa kamar MTN ko Etisalat su hada maka layin wayarka tare da abin hawanka, ta yadda idan baka kusa da ita za ta fada maka duk abin da ya faru da ita. Ko da kofa aka taba, nan take ba tare da bata lokaci ba za ta fada maka, wani abin mamaki ma za ta iya gaya maka wace kofa aka taba daga cikin kofofin motar.

Da za a yi rashin sa’a a dauke motar za ta gaya maka a daidai inda motar take lokacin da kake nemanta. Ko da yake masu karin magana suna cewa “Duk miyar da ta yi dadi, an kashe mata kudi ne”, ya danganta da irin kayan tsaro da ka sa wa motarka ko kuma daidaitawar da kuka yi da kamfanonin sadarwan. Domin idan kabiya isashshen kudi za a iya tsayar da motar a inda take.

Daga karshe, ita kanta wayar za ka iya sa mata wani application a cikin ta wanda zai dinga lura da ita kanta wayar ta hanyar amfani da internet, ta yanda in wani ya dauke wayar ya cire SIM din ka ya sa nashi nan take za ka samu sanarwa ta layin abokinka ko wani layin da ka sa idan an canza SIM din wayar a sanar da kai, za ta gaya maka SIM din da aka sa, da lokacin da aka sa da kuma wurin da aka s aka. ILLA IYAKA.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here