Bude mini Windows

Wani yaro ne yake aiki a Business Center sai wani mutum ya ga yadda yake yin aiki ya burgeshi shine yace zai kai shi wani kamfani a dauke shi aiki. Bayan lokacin yi mishi interview yaro ya dau wanka ya shiga wajen Interview, aka tambaye shi kasan computer, yace sosai sosai, ake ce bude windows. Yaron kawai sai ya tashi ya kama bude wundinan ofis din. Idan kaine ya zaka yi?

Get in Touch

  1. Ah ah, wai meye ne na kwafsi anan, ai cewa akai ya bude windows. wannan ai tambaya mai harshen damo. dama cewa sukai ya budo masu windows (BUDO MANA WINDOWS), anan kowa na iya fahimtar cewa na komfuta ake nufi. Amma Yaron really knows what he’s doing, ba laifin shi bane. Loooool

  2. Ai shi wananan yaron ya cancanci a bashi offer kai tsaye amma ta Masinja ba domin yaiya bude tagogi

  3. Mhn! Wannan ai laifin masu ganawa da shi ne wato (interviewers), da ba su fayyace masa wanne windows ba. Saboda haka don ya yi haka ba lefi ba ne a ganina amma a juri zuwa rafi…

  4. To, ka san yanzu mutane da yawa za su iya ‘operating’ comfuta ba tare da karatun ta ba. Kamar yadda muke da injiniyoyin da suka kware da kanikanci ba tare ma da sun iya ko da karatu da rubutu ba.
    Don haka a fassara masa abinda ake son ya yi yadda zai gane. Watakila ma ‘wizard’ ne a irin yadda yake.

  5. Kada kuga laifinsa kuma hakan da yayi ai shike nuna cewa yasan computer masu interview din sune basu san aikinsu ba domin in za’abude computer aiba mai kunnawa bane yake bude window ba sai ka kunna computer r ka sannan computer ka ta bude maka window 7 ko window xp din da ke cikinta. Don haka koda nine kace min bude window sai in bude maka .taga. Inkace bude computer sai in kunna maka computer ita kuma computer sai ta bude window din dake cikinta.

  6. Gaskiya wannan yaro ya kwabsa kwabsawama sosai ai duk wanda yake tu’ammali da computer yasan akwai computer language don haka tunda yasan cewa yazo wurin domin ita computar ai bai kamata ba yayi wani tunani wanda ba na computer ba, ni aganina wannan bai cancanta da ko masinja ba

  7. nima dai banga laifinsa ba domin cewa akayi ya bude windows… Amma da cewa akayi ya budo windows a gani…

  8. Salam. Allah yayi masa Albarka, yaro ya cika umarni, dominda motar biliyan goma da ta dubu dari duka sunan su mota, da catarpillar da taxi dukan su mota ce amman sai aka ban banta sunayen su. dasunce masabude mana window na kwamfitan nan sai ya bude CD-Rom to sai suce baisan abin da yakeyi ba

Leave a Reply to Halima Abubakar Cancel reply

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Get in Touch

19,710FansLike
2,180FollowersFollow
8,322SubscribersSubscribe

Latest Posts

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin...

Yadda Wayar Selula take yin aiki

Yawancin mu a wannan lokaci wayar hannu ta zaka bangaren rayuwar mu, amma kuma nasan daga cikin tambayar da muke bukatar amsarta shine wai...