Blackberry – Abubuwa guda 10 da mai amfani da ita ya kamata ya sani

0
2186

An ce kasar Nijeriya tana daga cikin kasashen da aka fi amfani da wayar hannu kirar Blackberry ba domin komai ba sai domin a farkon farawa mutane suna amfani da ita saboda isa da mallaka, wasu kuma suna amfani da ita saboda yin kuru da kuma neman a ce ina da ita. Wasu kuma sun sayi wayar Blackberry ne domin kawai zamani da kuma abubuwan da ake amfani da ita wanda ba kowace waya ba ce take bayar da irin tsarin shi ya sa suka mallake ta. Amma duk da haka sai na lura matuka bayan tsawan lokaci da na mallaki wayar Blackberry kuma tana hannuna amma kuma ban san amfanin ta ba. Sai dai kawai in amsa waya ko in kira, ko kuma aika da sakon SMS da dai kuma daukar hoto. Wannan dalili ya sa bayan na sami wani kanina yana da wayar Blackberry ya fada mini abubuwa masu amfani wanda na ga ya dace a ce duk mai wayar ya yi amfani da su kuma ya san su.

1) PIN lambarka da ke jikin Blackberry

Kowace Blackberry da muka ganta tana da wata lamba ta musamman wacce ta kebantu da ita wacce masu amfani da wayar suka sani da PIN Number. To, ɗaya daga cikin abin da ya kamata mu sani cewar wannan lambar ta wayar Blackberry da ke hannunka ne kawai kuma babu yadda da za a yi a canza ta. Koda kuwa ka canza wayar ko kuma ka canza SIM ɗin ka, to wancan PIN yana can waccan wayar.

Haka idan ka sayi sabuwar Blackberry abu na farko da ya kamata ka sani shi ne mene ne PIN dinta, sannan kuma yay a  za a yi ka gano lambar PIN dinta? Ya danganci wane irin Theme kake amfani da shi amma kusan ana samun inda za a ga PIN a wurin da aka rubutu Option a ƙarƙashin folda da ke fuskar Blackberry ko kuma ka shiga setting sannan ka shiga personal Identification a nan ma za ka iya ganin lambar wayarka.

Wani abu da mafi yawa daga cikin masu amfani da Blackberry ba su fahimta ba shi ne a duk lokacin da ka aika da saƙo ko da na mene ne, to ka sani kana amfani da wannan PIN lambar ne, haka kuma ko da kana browsing ko kana aikawa da email ne duk kana amfani da wannan lambar ne. kodayake ba dole ba ne ka san irin wannan bayanai amma kuma yana da matukar amfani ka san lambar Blackberry na abokanka da kuma waɗanda kuke yin hulda da su.

Idan ka san PIN number ta abokinka, to za ka iya aika mishi da saƙo kai tsaye ba tare da wani matsala ba. Duk lokacin da ka aika wa da wani mai Blackberry saƙo ta hanyar yin amfani da PIN ɗin shi, to sakon yana zuwa cikin sauri da kuma hanzari. Sabanin email wanda idan ka aika wa da wani sakon imel dole sai imel ɗin nan ya je zuwa ga kwamfutar wani sannan a aika da shi cikin akwatin wanda ka aika wa da shi. Irin wannan hanya da ake amfani da ita ta wajen aika wa da sakon daga Blackberry zuwa Blackberry kamar yadda ake da “PIN Message” ya fi kowane irin saƙo da mutum zai aika saurin isa. Shi ya sa a duk lokacin da ka aika da irin wannan saƙo da zarar sakon ya isa zuwa wurin wanda aka aika zai sa harafin “D” a gefen makin da ke nuna cewar sakon ya isa. Wannan harafi na D shi ke nuna maka cewar wannan sakon ya isa kuma wanda aka aikawa ya ga sakon.

2) Amfani da Setup Wizard lokacin farko

A lokacin da mutum ya sayi sabuwar Blackberry idan ya kunna ta abu na farko da zai fito a jikinta shi ne Setup Wizard. Shi setup wizard wata hanya ce da aka tsara wa mai amfani da wayar Blackberry domin  saukaka mishi wajen shirya yadda yake son ya yi amfani da ita wayar. Amma mafi yawa daga cikin masu amfani da ita wannan wayar sai ba su cika damuwa ba wajen su tsaya su cike tambayoyin da shi wannan Wizard ɗin yake yi. Rashin tsayawa a cike wannan Wizard ɗin na barin waɗansu gurabu da ya kamata a ce ka cire su ko kuma ka toshe su. Kamar duk lokacin da wayar Blackberry ta zo tana zuwa da yaruka da yawa da mutum baya buƙatarsu. To, idan a misalin kana son ka riƙa amfani da yaren Turanci ne, to a lokacin da wannan wizard ya zo ya tambaye ka wane yare kake so, ka zaɓi Turanci, to zai cire dukkanin ragowar yarukan da suke cikin wayar. Wannan ciresun da ya yi zai taimaka wa wayarka wajen rage mata nauyi da kuma kara maka girman ma’ajiyarka a cikinta.

Har ila yau a wurin shirya wayarka akwai abubuwa masu amfani da za ka koya kamar yadda za ka iya shige da fice a cikinta (Navigation) haka a wurin ne za ka iya shirya imel da kake son ka riƙa amfani da shi a ita wayar taka ta Blackberry.

3) Yi amfani da babban yatsa ba kumba ba

Ɗaya daga cikin kuskuren da masu amfani da Blackberry suke yi shi ne wajen yin rubutu da maɓallan Blackberry a lokacin da za ka samu mutum yana amfani da kumba wajen yin rubutu maimakon tafin babban dan yatsa. Yadda aka tsara maɓallan da ke jikin Blackberry an tsara su ne ta yadda komai faɗin babban ɗan yatsa zai iya hawa kuma ya yi rubutu ba tare da ka rubuta harafin da ba ka yi niya ba. Duk wanda yake ƙoƙarin kiyaye yin rubutu da tafin babban ɗan yatsan sa, to za ka samu ya fi saurin yin rubutu. Amma yin amfani da tsinin ɗan yatsan ko kuma yin amfani kumba na kawo rashin sauri ga mai rubutu.

4) Rage bata lokaci wurin amfani da AutoText

AutoText ɗaya ne daga cikin abubuwan da suke cikin Blackberry wanda suke saukaka wa wanda ya sani wajen yin rubutu. Domin AutoText shi wanda yake lura da mutum a lokacin da mutum yake yin rubutu a Blackberry. A misali a duk lokacin da mutum yake son ya rubuta kalmar can sai ya yi kuskure ya rubuta acn to AutoText zai canza ta kai tsaye zuwa can.

Haka shi AutoText yana ƙarawa mutane saurin yin rutubu saboda yana cike waɗansu alamomin da mutum yake buƙatar sai ya yi amfani da maɓallin alt kafin wannan alamar ta bayyana. A misalin idan mutum zai rubuta kalmar can’t dole sai ya latsa maɓallin alt sannan ya latsa maɓallin k kafin alamar ta bayyana. Wannan yana kawo cikas wurin yin rubutu da kuma nawa. A Blackberry duk lokacin da ka zo rubuta wata kalma wacce akwai alamar (apostrophe) a kanta ka rubuta shi ba tare da ka saka ba, da zarar ka ba maɓallin space zai saka maka wannan alamar.

Haka har ila yau akwai waɗansu karin abubuwa da AutoText yake yi fiye da wancan da muka ambata. Domin akwai waɗansu abubuwa da aka yi a Blackberry wanda za su kara maka sauri wajen yin rubutu. A misali sai kana rubutawa wani sakon imel sai kana son ya kira ka a lambarka. To, idan ka tashi rubuta lambar taka a cikin wayar Blackberry ba ka buƙatar ka rubuta ta. Abin da kake buƙata shi ne ka rubuta mynumber kana rubuta haka AutoText zai canza ya rubuta lambar wayarka a wurin. Haka idan kana son wani ya rubuta wa wani lambar PIN ɗinka na Blackberry, to a wurin sakon za ka rubuta mypin kawai shi kuma zai cire ya mayar da lambar PIN ɗin ka ne. sannan idan mutum yana son ka gaya mashi wane irin Blackberry kake amfani da shi a halin yanzu kawai za ka rubuta mishi myver wannan zai canza ya faɗi irin wacce kake amfani da ita.

Wadanann da muka ambata kamfanin da ya yi Blackberry ne ya tsara su. To, kaima da ka samu wannan wayar za ka iya shiga cikin AutoText ka tsara abubuwan da kake son idan ka rubutasu ga yadda kake son fito. A misali sai ya kasance kana yawan amsa tambayoyin mutane amma kuma wani lokacin abubuwa suna cakude maka ya zamanto ba za ka samu damar bayar da amsa a nan take ba. to za ka iya shiga AutoText ka kirkiri wani rubutu da duk sanda ka rubuta shi zai faɗi kamar haka. Misali ka rubuta llll sai ka rubuta na sami sakon amma a halin yanzu ina cikin uzuri nan gaba kaɗan za a sami amsa. To duk sandaka rubuta IIII to zai canza zuwa ga wancan maganar. Wannan zai taimaka kwarai wajen yin rubutu da sauri.

5) Ƙaramar hanya wajen yin rubutu (shortcut)

Ana amfani da ƙaramar hanya wajen yin rubutu a Blackberry kodayake wannan ƙaramar hanyar ba su da yawa, sai dai yana da kyau mai amfani da Blackberry ya san su domin ya samu saukin rubutu

  • Space bar: Wanda ya danna space sau biyu zai sa mashi alamar tsayawa na (.) a lokacin da yake rubutu
  • Riƙe maɓallin harafi: Wanda ya riƙe maɓallin harafi to harafin zai canza daga ƙaramin rubutu zuwa babban rubutu.
  • Rubuta adireshi a Intanet: Idan mutum yana rubuta adireshin wani gida da ke Intanet idan ya gama rubutawa sai ya zo inda zai sa alamar tsayawa idan ya danna maɓallin space sau biyu zai sa mishi alamar tsayawa ta (.)
  • Rubutun adireshen imel: idan kana rubuta adireshen imel a Blackberry inda za ka sa alamar @ to idan ka danna maɓallin space, to zai saka maka wannan alamar idan kuwa ka sake danna maɓallin zai saka maka alamar tsayawa.

Amma mu sani cewar wannan yana aiki ne kawai a Blackberry da kuma application dinta da wanda ya yi application ɗin ya bada wannan dama.

6) Ka sayi memory card

Yana da kyau wanda yake da Blackberry ya sayi ‘memory card’, domin amfaninsa a jikinta yana da yawa. Kasancewar memory da take zuwa da shi ba yawa gare shi ba, ga shi kuma kusan wayoyi suna da tsarin ba ka damar da saka hotuna da kuma sauti da bidiyo a cikin su. Idan ka ce za ka yi amfani da wanda yake cikinta, to zai kasance ya cika da wuri kuma idan ya ƙusa cika dukkanin tsofaffin kayayyakin da ka ajiye za su riƙa sharewa da kan su.

Shi ya sa yake da kyau ka sami memory koda ɗan karami ne ka saka mata domin yin hakan zai ba ka damar zubawa da kuma ajiyar isassun abubuwa a cikinta.

7) Ka yi amfani da Blackberry a matsayin wani ma’ajiya

Idan mutum ya haɗa wayarsa ta Blackberry ta USB da kwamfutarsa, to abu na farko da zai fito shi ne ya tambaye shi ko yana son ya yi amfani da Blackberry a matsayin wurin ajiya?. To idan mutum ya zaɓi e to Blackberry za ta bayyanar da kwakwalwar da take ajiyar abubuwan ka ta hanyar buɗe wani drive. Idan hakan ya faru zai baka damar da za ka iya ɗauko kaya kai tsaye da kwamfutar zuwa memory na wayar ko kuma daga wayar zuwa Kwamfuta ba tare da wani wahala ba. Sannan kuma ta wannan hanyar zai ba ka damar ka iya dibar abubuwa masu mahimmanci daga kwamfutar zuwa wata kwamfutar.

8) Ka saukar da  software na Blackberry (Blackberry Desktop Software)

Za ka iya yin amfani da Blackberry ba tare da wani software da zai taimaka maka ba kuma babu matsala. Amma amfanin wannan Blackberry Desktop Software yana da amfani matuka musamman ga wanda yake son ya yi waɗansu abubuwa da suka shafi amfani da wayarsa a matsayin hanyar samun Intanet ga kwamfutarsa. Domin kamar wanda ya sami damar shiga Intanet a wayarsa, to zai iya mayar da wayar ta koma a matsayin abin shigarsa Intanet (modem). Yadda idan kana son ka yi browsing a kwamfutarka ba sai ka nemi wani modem ba, to wannan software zai ba ka damar mayar da wayarka a matsayin modem sannan kuma ka iya shiga Intanet ka yi browsing kamar yadda kake yi da wayarka.

Haka ana amfani da wannan software wajen saka wa ita wayar sauti da bidiyo wanda a lokacin ɗaya daga cikin amfanin da yake da shi shi ne yana iya canza maka tsarin bidiyon ko sautin zuwa wani tsari na daban da Blackberry. Haka zai baka damar ka ajiye dukkan abubuwan da yake cikin wayarka zuwa cikin kwamfutarka. Tun daga sunayen cikin layin wayarka, da wanda yake cikin kan wayar, da sakwannin SMS da ka samu dama dukkan waɗansu abubuwa da suke kan wayar taka. Wanda daga baya idan wayar ta lalace ko ta bace za ka koma kan wannan application ka saukar da su.

Haka da wannan software za ta iya dubawa ka ga ko kamfanin Blackberry sun sake sakin wani sabon Operating System domin ya baka damar ya canza. Domin mafi yawan lokaci kamfanonin waya sukan canza manhajan wayarsu to, da wannan software kawai za ka iya mayar da ita Blackberry ta samu sabon manhaji.

9) Zuba wa Blackberry software masu amfani

Akwai waɗansu software ko kuma application masu amfani da mai Blackberry ya kamata ya saka su a cikin wayarsa, waɗannan application suna da yawa waɗansu kyauta ne waɗansu kuma na kuɗi ne. da farko dai idan kana son ka shiga gidan da ake samun irin waɗannan application da suke amfani a wayoyin Blackberry dole sai ka shiga gidan ajiyar application na su wanda ake kira da App World.

Da zarar ka buɗe ‘menu’ ɗinka za ka ga hoton da yake wakiltar app world wanda da zarar ka taɓa shi zai buɗe maka babban shafin nasu. Idan ka shiga zai nuna ma ga waɗansu dakuna kamar guda biyar wanda suka haɗa da dakin

  • Games, a wannan dakin ake samu application na wasanni
  • Apps, wannan daki ne da ake samun application kawai
  • Theme, wannan daki ne da ake samum themes (riguna) da za ka iya canza wa Blackberry ɗinka.
  • My World, idan ka shiga wannan dakin shi kuma zai nuna maka dukkanin application da ka riga ka sakasu a cikin wayarka
  • My Account, shi ne dakinka da za ka iya shirya yadda za ka sarrafa yadda za ka riƙa biyan kamfanin Blackberry kuɗi a lokacin da ka ga application na saidawa kuma kana son ka siya

10) Mayar da Blackberry ta koma taka

Haƙiƙa mutum zai iya mayar da Blackberry ɗin shi ta zama kamar tashi, an baka dama kamar kowace irin waya a Blackberry shi ma za ka iya canza theme da yadda kake son ka ga wayar ta zama yadda kake buƙata. Kamar canza sautin kira da sautin shigar sakon SMS da wani irin launi kake son idan an aiko maka da saƙo ya nuna maka ko kuma yaya kake son idan ka buɗe Bluetooth, wane irin launi kake so, da dai makamantansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here