Abubuwan Da ya Kamata Ka Sani Game Da Anti-Virus Software

0
1673

Idan ka bar na’urarka ba tare da ka tsareta daga miyagun Virus ba, abubuwa marasa kyau za su fara damun na’urar.

Anti-Virus Software mai kyau shi ne kawai maslaha ga dukkanin yamutsi da mugayen virus da suke damun computer da irin manyan wayoyin tafi-da-gidanka, irinsu Raila-Odinga da sauransu. Saboda haka, kada wata computer ta yi aiki ba tare da Anti-Virus ba.

Anti-Virus yana aiki ne ta wajen tace dukkanin na’urarka daga virus da worms ta hanyoyi guda biyu.

Kai tsaye ‘On-access’ da zarar ka kunna na’urar ka shi anti-virus din zai fara scanning ta karkashin kasa, ba tare da ka sani ba, zai bi dukkan kusurwoyin na’urarka ya bincika ya ga ko akwai bako wani cuta ko wani program da bai gamsu da shi ba ya cire shi, haka ma idan ka bude akwatin wasika wato email zai shiga ya duba ya gani ko akwai virus.
Wani lokaci, shi mutum ne da kan shi zai umarchi anti-virus din ya yi scanning babbar kwakwalwa ko kuma wata folder da kake so ya bincika ko akwai virus.

Ka tsare kanka daga sababbin Virus da suka shiga gari

Dukkanin wadannan Bangarori na bincike virus na iya ganin virus ne da abin da aka sanar da su cewar Virus ne (Defination), wato dukkan anti-virus yana iya gane cewar wannan virus ne, idan akwai bayanin shi wannan virus din a cikin computer. Shi yasa za ka ga idan aka sa wani abu acikin na’urarka mai virus, kamar USB Flash, Floppy Disk za ka ga anti-virus software ya gaya maka cewar akwai virus mai suna kaza, ga karfin da yake da shi wajen lalata na’ura, ga kuma irin Barnar da zai iya maka, sai ya tambayeka ya cire shi ne, ko ya gyara shi, ko ya ajiyeshi a wani wuri da ba zai iya cetar da na’urar ba, ko kuma kadama ya yi komai. ZaBi ya rage gareka.

To idan sabon virus ya shiga gari, ko aka sameshi a wajen canjin file daga wannan system zuwa wani system, ko kuma ta hanyar sakon email, to idan ba ka yi updating shi definition din ba to shi anti-virus din bashi da wani amfani. Saboda haka ya kamata karanci akalla sau daya a sati ka yi updating definition na antivirus din.

Wani abin murna! Wasu daga cikin sanannun anti-virus kamar su Norton da Kerspasky da irin su McAfee, sukan yi updating kansu da zarar suka fahimci akwai haduwa tsakanin na’urarka da internet (Connection).

To, amma idan kana amfani da anti-virus na kyauta (Free Anti-Virus) to, shi baya yin updating da zarar kana kan internet, dole sai ka ce was shi anti-virus din ya yi updating.
Kayi cikakken scanning yafi

Ka sa anti-virus ya yi scanning da kan shi ya fi kyau da kuma dacewa a kan shi anti-virus din ya yi scanning ta karkashin kasa. Saboda haka, yana da matukar muhimmanci kasa anti-virus ya yi cikakken scanning na computer dukkanta, sannan a ko da yaushe, kamar a kowane sati sau daya. Yadda ko za ka yi, za ka kunna anti-virus dinka sannan ka zaBi inda kake son ka yi scanning sannan latsa Ok ko makamancin shi.
Wadansu anti-virus software za ma ka iya ware wasu lokuta da za ka gaya mashi cewar kana son duk sa’adda wannan rana da lokaci suka zagayo, to, ya yi scanning din na’urar dukkanta, ba tare da ya shawarceka ba, ko kuma ma ya tuna maka cewar ka sani ya yi scanning a ranar, ya yi ko kada ya yi?

Yadda za ka yi idan Virus yafi Karfin Anti-Virus Din ka

Wani lokacin ko da ka yi updating definition na anti-virus a kan samu wani virus ya zama su kamfanin anti-virus dinka ba su samu maganin shi wannan cuta ba, saboda haka sai ya zama gashi kana da anti-virus kuma ka yi updating definition din shi ga shi kuma ya kasa cire maka virus din. To, idan haka ta faru, akwai wadansu kayan aiki (tools) wadanda suke iya cire irin wadannan virus, za su cire kuma su yi kokarin gyara duk wata Barna da virus din ya yi. Idan kuma aka yi rashin sa’a babu wannan irin kayan aiki, to, za ka iya shiga internet ka samu ka samu irin wadannan kayan aiki na kyauta da suke iya cire kowanne iri virus kyauta (duba http://securityresponse.symantec.com/avcenter ko kuma http://www.vil.nai.com/vil/avertools.asp).

Wani lokacin za ka ga saboda karfin virus din sai ya hana ka shiga ko kuma dauko irin wadannan tools din, to shi ma idan haka ta faru, sai ka sami computer wani, ko da abokin kane, ka sauko da wannan tools (downloading) ka kwafeshi a CD sannan ka mayar da shi cikin taka Computer.

Idan ita computer taki tashi saboda karfin virus din, domin sharrin virus yana da yawa, ka ga zai iya hana na’urarka tashi, ko ya hana ta hada ka da internet ko kuma ya hana duk wani program da ke da alaka da anti-virus aiki, ko ma yana asa ko a cire wani program. To shi ma idan haka ta faru, hanyoyi biyu ne, ko dai ka dawo da na’urarka zuwa lokacin da tayi aiki, zuwa lokaci da ita na’urar bata sami matsalar ba, ko kuma ka duba cikin kwalin da aka kawo maka na’urar akwai CD da ake kira recovery CD ko kuma ka tashi na’urar ta safe mode .

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here