ZAFAFAN WAYOYI 20 DA BA IRINSU

A wannan lokacin da muke ciki yana da wahala ka iya gamsar da mutane cewar waya iri kaza ta fi kyau ko ta fi inganci musamman idan ka yi la’akari da irin wayoyin da mutanen mu suke rikewa wadanda mafi yawansu kamfanoni masu tasowa ne suke yin su.

Irin wadannan wayoyin zaka samu sun fi yawa a hannun mutane talakawa iri na, kuma duk da cewar irin wadannan wayoyin suna iya biyawa mutum bukatarsa ta kira da shiga intanet. Amma kuma idan aka zo maganar fitattu da duniya ta san cewar an gina su akan tsari da ilimi, ta bangaren abin da ya shafi karfin batiri, camera, sensor da makamantansu sai ka samu cewar irin wadannan wayoyin da muke rikewa ko sunan su baya fitowa a cikin wayoyin hannu da ake takama da su.

Wannan jerin da zan kawo ya kunshi wayoyin komai-da-ruwanka guda a shirin wadanda suka yi tashe a cikin shekarar 2016 da kuma wata biyu da muke ciki a yanzu 2017. Duk da cewar zan yi kokarin ganin na kawo asalin kudadensu a kasuwa, amma kuma ba dole bane ya kasance kudin yayi daidai da yadda ake siyar da su a shagon da ka samu taka.

20 – BlackBerry Passport

Nasan wadansu za su iya kallon wannan wayar a matsayin zubin da, amma dai har yanzu matane su na son ta sosai. Tana da maballin rubutu a wajen (zahiri) kuma maballan an shirya su ta yadda mai amfani da su  zai iya yin amfani da hannaye guda biyu lokacin da yake yin rubutu, kamar yadda ake amfani da baban maballin kwamfuta. Kudin ta $200

19 – BlackBerry  Classic

Idan kai ma’abocin mu’amala da BlackBerry ne lallai  zaka so wannan wayarta BlackBerry Classic. Ta yi kama da tsohuwar BlackBerry, amma tana da ingantaccen fuska ga shi kuma fuskarta ana taba da hannu ne sannan kuma tana da maballai na zahiri. Kudinta $362.50

18 – BlackBerry  Priv

BlackBerry Priv ta banbanta da tsarin da aka saba ganin wayoyin BlackBerry suna zuwa da shi. Maimaikon ace ita wannan wayar tana amfani da babbar manhajar ta (Operating System) na kamfanin BlackBerry, sai  ya kasance ita Android Operating System ne a jikinta. Duk da tana kama da wayoyin Android amma kuma ana iya zaro keyboard na zahiri.

Wannan wayar masu son yin amfani da wayar da ke da maballin rubutu na zahiri kuma suna son su rika shiga google store zasu so ta sosai. Kudinta $370

17 – Moto G4

MotoG4 iri uku ce, akwai Regulr G4 kudinta $200 sai G4 Plus kudinta $250, sai G4 Play  wacce har yanzu ba a yi mata kudi ba.

Ita wannan wayar ta G4  Play  tana da 16-megapixel camara, wacce ita regular G4 13-megapixel, kuma tana da naurar tantance ‘yan yatsu fingerprint sensor wanda sauran kirar na G4 basu da shi. Wanda yake nuna cewar lallai wannan wayar ta hadu sosai

16 – Galaxy Note 5

In dai ana maganar waya mai babbar fuska to Galaxy Note 5 ba a cewa komai. Kamar yadda aka san wayaoyin baya na Note, ita ma wannan tana da kyakkyawan fuska da kuma kaimi wurin nuna kowane irin kala da kuma dadin aiki saboda itama taba ta ake da dan yatsa, ga shi kuma tsarin ginin karfe da tangaran da aka yi a jikinta sai ya kara mata kyau matuka. Kudinta $562

15 – ZTE Axon 7

Kamfanin ZTE ne suka yi Axon 7, wannan kamfani ne na kasar China wadanda suke hada wayar koda yake wannan kamfani ba sananne bane mafi yawan jama’a wurin kirkiran wayoyi sai dai kayan shiga internet.

Dalilin da ya sa muka kawota cikin wannan jerin saboda tana bayar da damar amfani idan muka yi la’akari koma muce tana iya fin mafi yawan wayoyin android wurin samun abubuwan da aka kirkire ta da shi. Zaka iya samu saunkin $250 idan ka hada ta da irin manyan wayoyi irin su Samsung, LG ko HTC.

Wannan yake nuna cewar idan baka son ka kashe makuden kudade wurin mallakar wayoyin da Nexus suke yi, kuma baka son ka siya mayoyi masu tsaka kamar Galaxy S7 ko HTC 10 to ZTE Axon 7 ita ta fi dacewa da kai. Kudinta $400

14 – LG G5

Wayar LG G5 an yi mata mazubin karfe ne gaba dayanta wanda ya sanya ake sonta sosai, sannan kuma ana iya budeta a cire batirin ta a canza da wani musamman idan batarin ya lalace ko kuma ya mutu. Kasancear ana iya bude wurin batirin ta kuma zaka iya samun damar kara wadansu abubuwa kamar karawa camera da ke jikin ta abin matso da hoto kusa ko nesa. Sannna zaka iya sa mata dual-lens (kara mata lens) wanda zai kara yaukaka hoton da zaka dauka. Kudinta $300

13 – LG V20

Duk da cewar ita ma tana da babbar fuska, sannan kuma tana iya baka damar ka iya aiki da dukkan wani app din da ka ajiye shi a favourite koda kuwa fuskar wayar a rufe take da kwado.

Abubuwan da ake yi ta da su suna da kyau matuka sannan kuma camera dinta ita ma haka, sannan bata da nauyi a hannu wurin rikewa ga shi kuma tana da karin wurin ajiyar bayanai na MicroSD, sannan ana iya cire mata batirinta itama. Kudinta $617

12 – HTC 10

Ba cewa komai idan aka zo maganar HTC 10 kasancewar ita wace da take da Android Operating System na asali wanda ba a taba shi ba wanda zai yi wahala ka samu tana da matsalar rikicewa ko kuma rudewa don an sa mata wani app a cikinta. Ba a maganar irin kayan da aka gina ta da su da kuma irin zubin camera da take da shi a jikinta. Kudinta $600

11 – Moto Z

Moto Z tana daga cikin wayoyin da suka fi kowace waya sirantaka, sannan kuma wayar ta hadu sosai domin kusan itama waya ce da ke zuwa da asalin Android Operating System da ba taba shi ba.

Ita wannan waya ta Moto Z tana zuwa da wadansu karin kaya da ake iya saka mata domin jin dadin amfani da ita ko kuma kara mata karko da karfi. Misali zaka iya kara mata speaker domin karfi sauti. Haka zaka iya kara mata na’urar projector ta waya domin kallon hotuna masu motsi a matsayin majigi a bango.

Ita wannan wayar iri biyu ce akwai Moto Z Force wace kamfanin Verizon suka yi. Idan ka hada ta da Moto Z ta kamfanin Motorola da Moto Z Force zaka samu ta fi ta girman fuska da kwari sannan tana babban batiri fiye da Moto Z da kamfanin Motorola suka yi. Kudin Moto Z $624, Moto Z Force $720

10 – OnePlus 3T

Bayan watanni biyar da kamfanin OnePluss ya fito da wayar OnePlus 3 sai kawai aka ji ya sake fitar da sabuwar waya OnePlus 3T. Abubuwan da ke cikin wannan wayar ba wai ya sabawa abin da ke cikin OnePlus 3 ba ne sai dai ‘yan kare karen da ba a rasa ba.

Sun karawa ita  wayar karfin gabatar da aiki ne ta hanyar karawa processor dinta gudu wanda OnePlus 3 tana da Snapdragon 820 ita kuma 3T tana da 821. Sannan sun karawa batirin girma kadan, sannan suka mayar da camera ta gaba ta koma 16-megapixel maimakon 8-megapixel da OnePlus 3 take da shi. Kudinta $440

09 – iPhone SE

iPhone SE fuskarta ta kai lanci 4-inc, ita ce wayar tafi-da-gidanka da babu kamar ta wurin siya a wancan lokacin. Zaka samu manhajojin masu kyau a jikinta da irin manhajojin da suke lura da lafiyar waya ecosystem, haka kuma idan ta samu wani matsala ana samun taimako ba kai tsaye. Kuma yadda iPhone 6S take yin aiki haka itama take yin aiki.

Sannan tana zuwa da Apple Pay da wadansu manhajoji na saidawa kamar su Live Photo kyauta da na’urar tantance ‘yan yatsu, bama a maganar yadda batirin ta ke dadewa sosai. Kudinta $399.

08 – iPhone 6S

Itama iPhone 6S abin so ce, domin tana zuwa da app a sayarwa kyauta a cikinta. Bayan kuma hardware masu kyau da aka gina ta da shi, sannan kuma duk wanda yake da ita yana da garantin duk wata manhaja da wasu suka yi na kyauta su fara samu, sannan kuma kodawane lokaci akwai updates na ita OS dinta da ma application da suke cikinta daga Apple. Kudinta $520

07 – iPhone6S Plus

Da yake yanzu iPhone 7 ta shigo kasuwa, ana samun ragin $100 a farashin farko na iPhone 6S Plus. Duk da ba zaka samun karin tagomashi da iPhone 7 take da shi a iPhone 6S Plus ba, kamar kariya daga ruwa, dual-lens camera. Amma iPhone 6S Plus ba a magana wurin tsari da kyau.

Tana amfani da A9 chip a jikinta wanda yake baka damar amfani da tsari irin na 3-D Touch, sannan tana da na’urar tantance ‘yan yatsu, sannan akwai manhajar Live Phone wanda zai baka damar daukar hoto na dakika uku tare da sauti a jikinsa kyauta. Kudinta $650

06 – Samsung Galaxy S7

Baya da kyakkyawan jiki da tsari da aka yi mata wurin kirkiranta, Samsung Galaxy S7 ita ce wayar da har yanzu ba a samu wata waya dake da camera da ta fita ba. Domin har ta fi iPhone 7 Plus a wurin karfin camera, ga shi kuma ruwa baya bata ta.

Sannan a jikinta akwai manhajar Samsung Pay wanda yake yin aiki a kusan kowane irin abu murum ke son ya siya a Samsung Store, irin abin da iPhone’s na Apple ba sa iya yi.

Amma wannan ba Galaxy Note 7 ba ce wacce aka sani tana kamawa da wuta a dalilin batirinta. Kudinta $503

05 – Samsung Galaxy S7 Edge

Ita Galaxy S7 Edge tana da babbar fuska mai girman lanci 5.5-inch sannan batirunta ya fi na Galaxy S7, amma dai kusan gininsu iri daya ne, kamar ruwa baya lalata ta, tana da MicroSD sannan akwai Samsung Pay. Kudinta $603

04 – iPhone 7

Ko shakka babu wayar iPhone 7 ta zo da wadansu karin tagomashi na manhajoji da kuma manhajar lura da lafiyar wayar ecosystem ga masu amfani da ita. Zuwan ta da ecosystem na nufin samun taimako kai tsaye daga kamfanin Apple duk lokacin da wayar ta samu matsala ko ta rikice, haka wayar zata samu update kai tsaye daga kamfani Apple duk lokacin da suka saki wani update.

Tana da banbanci tsakaninta da iPhone 6S domin tana aiki sosai da wadansu kayan da kamfanin Apple suke kerawa kamar AirPods wanda na’urace ta sauti da ba a sa mata waya a jikinta (wireless). Sannan kuma ruwa baya lalata ta, sannan an sake inganta camera dinta ta yadda take iya daukar hoto tangaran koda yana cikin inda babu haske sosai a wurin, sannan tana da na’urar tantance ‘yan tsasu sannan kuma na sake gyara hanyar da signal na network ke shiga cikinta. Kudinta $650

03 – IPhone 7 Plus

iPhone 7 Plus zuwan da tayi da karin dual-lens camera shine abin da ya fara dararwa iPhone 7. Domin wannan yana baka damar daukar hoto kamar gogaggen mai daukan hoto, wanda ake iya bata bayan hoton a fito da zallan abin da ake son a dauka kawai. Shi kuwa dayan lens din yana da tsarin telephoto lenswanda yake da damar zuko hoto kusa kusa, wanda yake nuna cewar koda an matso da hoton kusa sosai, kyau na hoton ba zai lalace ba kamar yadda sauran camera na wayoyin tafi-da-gidanka suke yi ba. Kudinta $769

02 – Google Pixel XL

Wannan ita ce wayar da kamfanin Google suka fara yi wacce take kunshe da kusan duk kayan karafan dake cikinta su suka yi. Sabani da sauran wayoyin da kamfanin google suke yi irin na Nexus wanda ba su suke yin hardware din ba.

Jikinta an yi shi da alminium ne hade da gilashi ta bayan ta kuwa akwai na’urar tantance ‘yan yatsu. Camera da take jikinta tana kafada da kafada da na’urorin daukan hoton iPhone 7 Plus da Samsung Galaxy S7, sannan manhajar HDR tana gyara hoto ya fito da ban sha’awa.

Babbar Google Pixel XL tana da fuska mai girman lanci 5.5-inch, abin da ya bananta ta da karamar ta ke nan. Ba kamar yadda sauran kamfanoni  irin su Apple suke banbanta babbar wayarsu da karamar ta ba. Kudinta $769

01 – Google Pixel

Google Pixel ta amfani da Snapdragon 821 wanda ya bata karfin sarrafa abubuwan da ke cikinta, tana da 4GB na RAM, sannan tana da 12.3-megapixel na camera wanda ya fi na iPhone 7 Plus da Samsung Galaxy S7.

Ba ta wannan bangarenta tana daga cikin wayoyin da suke da saurin dibar wuta sannan tana da fuska mai kyau, sannan tana amfani da Google’s Pixel laucher wanda yake ba Android damar ta tashi ba tare da matsala ba. Kudinta $649

4 COMMENTS

  1. Gaskiya munajin dadin wannar hanya ta ilmantarwa.
    Amma abinda nakeso nayi tambaya anan shine, menene bambancin manhajar android da aka chanja mata tsari da wadda baa chanjaba..?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here