Yadda dawo da lafiyar Nokia E66 cikin ruwan sanyi

5
2025

Wannan dan bayani zai taimaka wajen wadanda suke tambaya akan yaya zasu iya dawo da lafiyar wayar su ta nokia a lokacin da ta samu matsa kamar yadda daya daga cikin daliban wannan dandalin mai albarka yayi kamar haka: Webmaster, da fatan kana lafiya.
Dan Allah wayata ce na manta security code dinta, Nokia ce kirar E66 to ina bukatar yi mata formating amma abin yaki yuwuwa.
Shi nake so ko akwai wani taimako da zan samu daga gare ka, inna dauko applications basa installation kuma wasu apps din ma basa remove kwata-kwata.

Ka huta lafiya. http://www.facebook.com/abdullah.nuhu

1. Gyara mai sauki (Soft Reset)

Wannan hanya ta share dukkan wani abu da aka sakawa ita wayar a cikin fallanta na .ini amma kuma baya goge abubuwan da ka saka a cikin ita wayar kamar su hotuna ko bidiyo ko rubuce-rubucenka ko kuma wani application da ka saka mata, zai yi kokarin ya dawo da ita zuga ga lafiyarta. Zaka rubuta *# 7780 # .

2. Kankare ta gaba dayanta (Hard Reset).

Shi kuwa nan kankare ita wayar ta koma babu komai a cikin ta, domin yana share dukkanin abubuwan da aka taba saka mata ta dawo kamar yadda aka sayota daga kamfani amma yana da kyau wanda yake son ya gabatar da wannan tsari ya tabbatar da cewar batirin wayar a cike yake, ko kuma yana hade da wuta, sannan ya tabbatar da ya kwashe dukkan abubuwa masu amfani a cikin wayarshi kamar hotuna da makamantansu. Bayan ya gama sai ya rubuta wannan a wayar ta shi. *#37370#

Wannan shine a takaice bayani akan yadda zaka yi resetting na wayar nokia E66.

5 COMMENTS

  1. Rankayadade ko akwai yadda zan iya toshe wani web address da banaso narika shigarshi kamar address din sport kona football, ma anadai nasamu narufe webdin tayadda konaso budeshi akan wayata shafin bazai budeba, dan budeshi yana cinye min lokaci.

  2. Salam inai muku fatan alheri, da fatan kuna lafiya (ALLAH) yasaka muku da alkhairi, Nidai tambayata in zan bude website ya zanyi nabude sai anjima ku huta lafiya .

  3. salam webmaster. Allah ya albarkaci wannan makaranta tamu mai daraja. Hakika muna matukar amfanuwa da wannan ilimi da kuke bamu a kyauta: amma fa ladan ku na wurin Allah.

    1. Don Allah ku fada min yadda zanyi FORMATTING DELL COMPUTER cikin sauki.
    2. menene bambamcin CACHE da COOKIES.

    nagode.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here