Ya kamata in damu da Computer Hackers kuwa?

Kalmar Hackers ta wayaita a bakin samari da ‘yan mata masu harkar tafiyar da kuma sarrafa computer a wannan zamani, wannan kalma ta yawaita a kusan kowane lungu da saƙo na duniya, kasantuwar yadda kowa ya ɗauki wannan kalmar, amma a yammacin duniya da kuma Nahiyar Turai kowa na jin tsoron hackers kuma ba ya son a jingina ita wannan kalmar a gare shi. Hasalima duk wanda ya san cewar computer shi bata da ingantaccen Antivirus software a cikin babu abin da yake ji ma Kwamfutarshi tsoro kamar Hackers!

Su waye Hackers a ilmance?

Za ka ji da zarar mutum ya san computer ko kuma ya iya sarrafata sosai sai ka ji ana kiran shi da kalmar harcker. A gaskiya kalmar “hacker” tana da ma’anoni da dama da kuma fassara iri-iri, amma idan aka dawo a kan harkar da ta shafi computer kuma kana son ka yi maganar hackers da computer to bai wuce ta ba su ma’ana guda biyu ba waɗanda su waɗannan ma’anoni biyun duk kana buƙatar saninsu. Kamar yadda aka fasara kalmar hacker a wani dictionary mai suna “Merriam-Webster” “Hacker ƙwararren masanin ilimin sarrafa computer (programmer). Shi kuwa wannan ma’ana da suka ba da ta ƙunshi kusan mutane da dama masu amfani da computer amma kuma waɗanda ba a tunanin za su iya cutar da wani.

Amma ma’ana ta biyu tafi tayar da hankali matuƙa, domin Hacker shi ne mutumin da ya shiga cikin Kwamfutar mutum ta ɓarauniyar hanya domin ya saci wasu muhimman bayanan shi ko kuma ya yi maka ta’adi”. Idan muka fuskanci wannan ma’ana ta biyu yana nuna mana cewar dukkanin wani abu da hacker yake ƙoƙarin yi shi ne ta’addanci tare da Kwamfutar mutane ta hanyar da kuma ɓarna, domin ha kan na faruwa ba tare da sanin mai amfani da Kwamfutar ba.

Yaya Hacker suke yin Hacking?

Ɗaya daga cikin hanyoyin da hackers suke yin amfani da ita domin su iya shiga cikin Kwamfutar mutum shi ne ta yin amfani da Malware. Malware wani ɗan ƙaramin software ne ko kuma program da ake sa ran zai iya ɓarka dukkan wata kariya a cikin Computer domin ya yi ta’adi.

Wasu hackers sukan ƙirƙiri waɗansu ƙananan program domin nishadi wanda a jikin wannan ɗan ƙaramin program ɗin sai su saka mishi ɗan ɗaramin malware domin shi wannan malware ɗin ya riƙa yin ɓarna a cikin computer ba tare da mai Kwamfutar ya sani ba. Wasu kuma waɗanda mugunta suka saka a gabansu sai su ƙirƙiri malware wanda shi babu abin da yake yi fa ce ya tattaro muhimman bayanai da kake rubutawa ko kuma ka ajiye a cikin Kwamfutarka, daga bisani sai ya maidowa da wanda ya yi shi waɗannan bayanai, shi kuma da wannan bayanai zai yi amfani wajen shiga Kwamfutarka har ya sa ce maka kuɗaɗenka da kuma wasu muhimman kayanka. Irin waɗannan malware waɗanda suke satar kalmomin sirrin mutum (password) ko kuma dukkan wani maɓalli (keyboard) da ka latsa suna ɗaukar shi suna aika wa hackers ana kiranshi da “keylogger”.

Yaya ake Malware yake shiga Kwamfuta?

Mafi yawacin malware da suke shiga cikin computer mutane ba su sanin lokacin da suke shiga. Wannan kuwa yana faruwa ne a lokacin da ka shiga internet domin yin downloading wani abu ko kuma ka duɗe saƙon imel da a cikinshi akwai malware tare da shi.

Shi malware sau tari yana zuwa ne a saƙon imel da ba ka san wanda ya aiko maka da shi ba, ma’ana mafi yawancin saƙo na banza da wofi da soki burutsu (junk ko spam) da ake aikowa da shi su suke tattare da malware. Haka Malware yana iya shiga Kwamfutar mutum idan mutum ya shiga website domin yin downloading, kawai abin da hackers suke so shi ne da zarar ka latsa link domin duɗe wani shafi ko kuma saukar da wani abu sai malware ya faɗo cikin computer kawai, ba tare da ka sani ba.

Me zai faru idan Kwamfuta ta ta faɗa hannun Hackers?

Matsalar guda ce yana da wahala a iya gane wane ne ya ƙirƙiri malware da ya yi ta’adi a Kwamfutarka, kodayake wani lokaci hukumomin sukan yi bincike mai zurfi har su gano wanda ya ƙirƙiri shi wannan malware ɗin. Sai dai idan har aka yi rashin sa’a ka faɗa hannu to babu wanda zai gyara maka ita Kwamfutar sai dai kai ka cire kuɗi daga naka aljihun ka biya, idan kuwa kwashe maka kuɗi aka yi, to babu wata hukuma da za ta ɗauki alhaki. Shi ya sa make da muhimmanci ka san yadda za ka bi ka hana Hackers shiga kwamfutarka.

To yaya za a yi in tsare Kwamfuta ta daga Harckers?

Hanya mafi inganci da za ka bi domin kare Kwamfutarka daga matsaloli irin wannan shi ne ka ɗaura wa Kwafutarka software waɗanda aka yi su musamman domin lura da malware, ko kuma waɗanda suke tare malware idan ka shiga website ko kuma ka duɗe imel da ba ka amince da wanda ya aiko maka da shi ba. Waɗannan program ba waɗansu ba illa ant-virus software ko kuma anti-malware software. Mafi yawan irin waɗannan software ba su da tsada kuma suna da sauƙin sakawa a cikin computer kuma kamfanonin suna ƙoƙari matuƙa wajen lura da irin waɗannan cututtuka da suke iya shiga Kwamfutar mutum. Su waɗannan anti-virus software suna iya binciken kwamfutarka su gano maboyar malware ko virus kuma su fitar da shi ba tare da kai mai Kwamfutarka sani ba. Saka irin waɗannan anti-virus software na da kyau mutum ya lura ko ma ya sani cewar arha bata ado, kuma mafi yawancin anti-virus na kyauta ko kuma waɗanda ba su shahara ba ba su iya kare Kwamfutarka, ko kuma wasu ma sukan ko ma makamin da su hackers suke amfani da shi wajen shigowa computer. Ka saka sanannen anti-virus, kuma shahararre, sannan wanda kuma yana da ilimin virus sama da miliyan tara, domin tsa kanin virus da Trojans da malwares ana da sama da miliyan tara da wani abu

Daga ƙarshe muna son ka sani kai mai karatun Hackers gaskiya ne kuma suna nan suna ƙoƙarin yadda za su yi su kifar da kai da kuma Kwamfutarka, saboda haka sai mu yi hattara!

BAR AMSA

Yi sharhin ka
Shigar da suna a nan