Tsakanin Muhammadu BUHARI da Jama’a

Buhari ba zai kara kwana daya da aka rubuta masa tun kafin a yi duniya ba. Haka kai ma da kake kokarin ganin ya mutu ko mulkinsa ya lalace kai ma ba zaka kara kwana daya ba. Da ace akwai wanda zai dawwama a nan duniya da Manzon Allah SWA da yana nan bai mutu ba.

Ita kanta mutuwar akwai ranar da zata mutu, to me ye na wani yin rige-rige na wai wane ya mutu?

Babban abin da ke bani tsoro shi ne addu’a da zaka ji wasu mutane suna yi domin wani matsala da ke tsakanin su da wannan gwamnati, irin addu’o’in da suke yi su sani yana dawowa kawunan su ne. Hakika Allah ya ajiye wadansu mala’iku da ba abin da suke yi sai maimaita addu’a da bawa yake yiwa bawa a kansa.

Misali da wani bawa zai kalli wani ya ce Allah ka wulakanta wane, to suma mala’iku zasu ce Allah ya wukanta ka. Haka da zaka ce Allah ta taimaki wane to kai ma mala’iku za su ce Allah ya taimake ka. Sai mu gani da addu’ar ka da ta mala’iku ta wa zata karbu?

Ina mamakin musulmin da ba shi da wani tunani sai ganin idan Buhari ya mutu shi ke nan komai ya lalace ko kuma mun shiga uku mun lalace. Wannan ba shi bane tunanin mu gare shi lokacin da ya ke neman kujera muke ta fadin cewar idan ba Buhari ya hau kan mulki ba komai zai komai zai koma daidai? Daga masu ikirarin Ahlussunna da wadanda ba su ba suka manta da cewar Allah shi kadai ya san wanda zai gyara da wanda ba zai iya gyara ba.

Kadan daga cikin jama’a ne kawai suke danganta kyautata da zaton Buhari zai kawo gyara a kasarnan, amma wadansu gani suke yi in dai Buhari ya hau mulki komai ba zai tafi daidai ba. Na tuna lokacin da Muhammadu Buhari ya je yakin neman zabe Maiduguri na ji jama’a a wurin suna cewa BUHARI CECE Mu, Allah shaida ne nace Allah zai jarrabe mu, domin muna neman taimako a wurin gajiya yaye.

Ba ma ganin wannan shi ne dalilin da Allah Ya hana mu mu ji zakin wannan mulkin da ake tunanin zai kawo karshen matsatsi da wahala da ake fama da ita kafin ya hau kan wannan kujerar?

Ina mamakin musulmin da yake yarda da wani pasto ko bokan dan duba da ya ce wai an nuna mishi wani nasara ko musiba da zata faru a cikin wannan gwamnatin har kuma yake yadawa a cikin shafinsa ko a wurin zamansa.

Ina son mu sani cewar duk abin da ya faru kafin halittar mu mu Allah Ya san shi. Haka wanda ya ke faruwa a yanzu shi ya shirya shi kuma ya tabbatar da shi. Wanda ma zai faru nan gaba ya na sane da shi da lokacin da zai auku. To mene ne na wani surutai.

Ni dai na yi imani Allah ba shi da abokin shawara idan zai gabatar da al’amari, haka ba shi da mata ballantana ta tilasta shi don jinkirta wani abu. Ba shi da dan da zai zo ya yi masa shgwabar da zai fasa yin wani al’amari.

Saboda haka idan Allah ya rubuta cewar Buhari zai shekara 8 a mulki ko ba yardar kowa sai ya kai wannan lokacin, haka idan lokacin sa ya kai koda ranar sake zabansa ne zai wuce.

Ballantana wani yayi tsammanin addu’arsa ce ta sa shugaba Buhari ya rayu ko ya mutu. Kai da kake tunanin idan 2019 ta zo zaku yi kaza ta ka bari ka kai lokacin cikin kwanciyar hankali hankali da lumana, sannan kuma kana da rai da lafiya?

Ni dai abin da na sani Muhammadu Buhari mutumin kirki ne kuma yana iya kokarin sa wurin ganin ya kyautatawa mutanen da yake shugabanta.

Ya samu nasara a cikin abubuwa da yawa kuma yayi kurakurai a cikin wadansu abubuwa amma a abin da ya bayyana gare mu mu yan adam masu kyautata masa zato daidai ya fi kurakuransa a mulki.

Amma idan muna son mu ga komai ya gyaru sai mun tabbatar da mun gyara kawunan mu, da yadda muke mu’amala da jama’a. Idan an sami dan Arewa da ke murnar rashin lafiyar Buhari to lallai dan kuma min babi aula.

Allah muke roko da ya bashi lafiya da nisan kwana da juriya da hangen nesa, da masu bashi shawara na gari. Ya baiwa marasa lafiya da suke gida ko asibiti ko masu tafiya da shi lafiya, idan kuma jinyar ba ta tashi ba ce Allah ya sa su yi shahada.

Salisu Hassan Webmaster
07.02.2017

4 COMMENTS

  1. Agaskiya maigida Salisu kaSan mutane kowa da irin tunaninsa Amma Allah yace kafadi alkheri kokayi shiru. Amma duk Wanda yakeda da wata mummunan munufa akan M. Buhari Allah zai mayar masa da munufarsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here