Shafin Sada Zumunta Na Facebook

0
780
A smartphone user shows the Facebook application on his phone in the central Bosnian town of Zenica, in this photo illustration, May 2, 2013. Facebook Inc's mobile advertising revenue growth gained momentum in the first three months of the year as the social network sold more ads to users on smartphones and tablets, partially offsetting higher spending which weighed on profits. REUTERS/Dado Ruvic (BOSNIA AND HERZEGOVINA - Tags: SOCIETY SCIENCE TECHNOLOGY BUSINESS) - RTXZ81J

Rubutawa: Bashir Ahmad

Sunan Facebook ba ɓoyayye ba ne ga matasan wannan zamani maza da mata, musamman masu mu’amala da fasahar ziyarar intanet. Domin kuwa ko da mutum baya amfani da shafin ba zai ka sa jin masu mu’amala da shi suna zancensa ba.

Duk da dai ba duk aka taru aka zama ɗaya ba, wato dai ba za a rasa ‘yan tsirarun mutanen da ba su san wannan shafi na Facebook ba, ko kuma idan sun san shi ba su san wa ce irin mu’amala ake da shi ba, kai wasu ma suna amfani da shafin amma ba su fahimce shi ba, domin kuwa idan za ka tambaye su mene ne amfanin Facebook, ka ba su aiki ba ƙarami ba. To idan kana ɗaya daga cikin wanda ba su san mene ne Facebook ba ko kuma kana ɗaya daga cikin waɗanda sun sanshi amma ba su san amfaninsa ba, kai har ma da waɗanda suka san shafin kuma suka san amfaninsa ku ɗan bani hankalin ku na ɗan lokaci don sanin mene ne Facebook, wa ya ƙirƙire shi, don me aka ƙirƙire shi, mene ne amfaninsa da sauran batutuwa makamantan ha kan.

Facebook dai dandali ne na sada zumunta kuma yana ɗaya daga cikin miliyoyin shafukan da ke kunshe a rumbun intanet wato Internet. Wato kamar irinsu shafukan Twitter, MySpa ce, Google+ da sauransu, sai dai shafin na Facebook ya banbanta da shafukan da na bayyana a sama ta hanyoyi da dama. Facebook shafi ne da wani ɗalibi mai suna Mark Zuckerberg ya ƙirƙire shi tare da wasu abokankaratunsa su uku Eduardo Saverin, Dustin Moskovitz da kuma Chris Hughes. A ranar 4 ga watan Fabrairu, 2004. A makarantar Harvard a jihar Califonia da ke ƙasar Amurka. Waɗannan ɗalibai sun ƙirƙiri shafin ne don amfani da shi a makarantarsu kawai, don haka cikin dan lokaci ƙanƙani shafin ya baibaye ilahirin wannan makaranta, saboda irin farin jinin da shafin ya samu a wurin ɗaliban makarantar Harvard ba’a dau lokaci mai tsawo ba shafi ya tarwatsu zuwa sassan manyan makarantun ƙasar Amurka baki ɗaya.

Kafin ka ce me tuni shafin ya tsallaka zuwa ƙasashen Kanada da Ingil, wajen shekarar 2005 shafin ya karaɗe gaba dayan yankin ƙasashen Turawa da yankin Amurka ta kudu. A ranar 26 ga watan 9 na shekarar 2006 kamfanin Facebook ya bayyana cewar kowa zai iya mallakar shafin a duk inda yake a duniya in dai ya haura shekaru 13 da haihuwa.

Shafin Facebook shafi ne da kowa zai iya amfani da shi cikin sassakar hanya, shafi ne da masu amfani da shi ke samun damar haɗuwa da mutane kala-kala daga ƙasashen duniya daban – daban, shafin yana da ƙayatarwa, nishadantarwa, ilimintarwa, shagaltarwa har ma da wa’azantarwa. Shafi ne daya haɗa al’ummomi kala – kala mabanbanta ra’ayi, ƙabila, addini, yare da kuma tarbiyya. Haka ya sa duk irin manufar da ta sa mutum amfani da shafin yake samun ‘yan uwansa.

Facebook wani dandali ne daya ba wa masu amfani da shi dama wurin baja kolin ra’ayinsu, ba tare da tsangwama ko hana ‘yancin magana ba, wannan dalilinsa Facebook ya tsere wa dukkan wani shafi na sada zumunta wato Social Network a Turance yawan masu amfani da shi. Kamar yadda kamfanin ya shaida cewar yana da sama da mutum biliyan masu amfani da shafin a ƙiyasin da aka yi a watan goma na wannan shekara ta 20121.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here