MECE CE COMPUTER?

Wannan maudu’an da zamu tattauna a wannan mujalla madu’ine mai fadi wanda yake bukatar tsawon lokaci wajen warware shi ko kuma dogon bayani wajen yin maga akanshi.

Da farko dai  ina so mai karatu ya sani cewar ita computer tana da ma’anoni da dama, wadanda kusan kowane ka dauka lallai zai warware maka tunani ko kuma neman sani dagane da ita computer.

TO MECECE COMPUTER? A CIKAKKIYAR MA’ANA

computer wata naura ce da take aiki da wutar lantarki ko batir, ana iya sarrafashi a sakamakon wasu umarni da ake ajiyesu a memory nata. Sannan kuma za ta iya karbar “Data” a matsayin abin shiga (input) sannan kuma ta sarrafa (Processing) wannan Data da aka saka mata kamar yadda ake so, sannan kuma ta fitar da sakamako (output), sannan kuma za ta iya ajiyar wannan sakamakon don gobe, ko idan bukatar hakan ta taso nan gaba.

Saboda haka ne, za mu iya cewa idan muka dauki wannan bayanai dangane da yadda computer take, shine dukkanin kayan nasara da ba zai yi aiki ba sai da wuta ko batir a matsayin computer, wannan ya hada da injin nika, T.V, radio, video, microwave, calculator, handset da dai makamantansu. Sai dai idan kuma muka dauki bayani na gaba zai cire mana wasu kayan da muka lissafa, shi ne da aka ce ita computer tana iya karbar sako wato ba kasancewar wuta na shiga cikin ta ba kadai, a’a za ta iya karbar sako, wanda ya kama kamar kowane irin rubutu, ko bayanai, ko hotuna, ko video ko me dai ake iya saka mata, to kaga a nan calculator, da wayar hannu sun shigo ciki tunda ana iya saka musu bayanai kuma su rike.

Sai dai ba a nan gizo ke sakar ba, har ila yau, ba wai karbar Data kadai take yi ba,  ita computer tana iya sarrafa wannan Data da aka saka mata kamar yadda aka umarceta, wato idan aka saka mata abu aka ce ki maimaitashi sau kaza to ba za ta kara ba ba kuma zata rage ba.  Sannan kuma tana iya fitar da sakamakon shi wannan bayanai da aka saka ta sarrafa, kodai a waje ko kuma a jikin ta, bayan tayi hakan za kuma ta iya ajiye wannan Data ko information da ake saka mata domin gobe ko kuma domin bukatar tashi in ta zo a nan gaba. Shi yasa kusan computer ba ta iya cika computer sai idan tana iya yin abubuwa guda hudu (4) wanda idan machine yana iya yin uku ko biyu daga ciki to bata cika computer ba, wadannan abubuwan sune:

 1. Ta iya karbar sako (input)
 2. Ta iya sarrafashi (Process)
 3. Ta iya fitar da shi (output)
 4. Sannan ta iya ajiyar shi (Storage), wanda a turance ake cema shi Information processing cycle.

To a cikin karatunmu ina ta maimaita kalmar DATA a ilmin Computer Science idan aka ce Data ana nufin: DATA itace dukkan dukkan abinda ake iya sawa computer a cikinta wanda basu da ma’ana, wanda suka shafi  kalma, ko sauti, ko hotuna, ko lambobi, sannan kuma ba a shirya su ba. Sabo da haka ne idan ka saka su a cikin computer, sai computer ta sarrafa su su zama bayanai (information).

Wanda yake anfani da computer a turance ana kiranshi da USER. Duk idan ka karanta wata mukala da turanci ana maimaita Kalmar User to ana nufin wanda ya ke yin amfani da kayan computer ya sarrafa ta. Sannan kuma karafuna ko kuma kayayyakin da ka ke amfani dasu wajen sarrafa ita computer su ake kira da HARDWARE, sannan kuma abubuwan da suke sarrafa shi Hardware har kayi amfani da su  su ake kira da SOFTWARE. Shi yasa computer take da manya manyan kayan sarrafawa guda biyu:

 1.  Hardware
 2.  Software

MENE NE HARDWARE?

Hardware shi ne dukkan abubuwan da kake iya gani tare da computer sannan kuma zaka iya tabawa. Wanda suka hada da Monitor (wato wannan abu mai kama da TV da ka ke gani), sannan Keyboard (wannan shimfidadden allo wanda yake da maballai da ake latsawa idan ana so ayi rubutu a cikin computer), sannan akwai Mouse (shi kuma wani dan karamin abu ne wanda zaka ga masu amfani da computer suna rike shi suna mommotsa shi da dai makamantansu, dukkansu Hardware ne saboda kana iya gani harma ka tabasu.

MENE NE SOFTWARE?

Shi kuma software shi ne wasu irin rubuce rubuce ne da ake yi ko kuma muce tarin umarni ne(program)da ake saka shi a cikin computer domin ya baka dama ka iya sarrafa Hardware, ko kuma ya gayawa computer abinda ya ake son tayi, shi yasa Software yake da matukar muhimmanci akan Hardware domin ba domin wadannan rubuce rubucen da ake yiba da babu yadda zakayi ka iya sarrafa computer ko kuma idan ka latsa maballi a jikin Keyboard har computer ta gane me ake so tayi.

KAYAYYAKIN COMPUTER (Computer Components)

Kamar yadda muka fadi cewar shi Hardware shi ne duk abinda za ka iya ganin shi a jikin computer kuma ka iya taba shi, sabo da haka shi Hardware sun kasu kashi biyar.

1)     Abin shigarwa (input devices)

2)     Abin fitarwa (Output Devices)

3)     Abin sadarwa (Communication Devices)

4)     Abin ajiya (Storage Devices)

5)     Gidan Computer (System Unit)

Me ake nufi da Abin shigarwa? (Input Devices)

Duk inda ka ji an ce Input Devices ana nufin kayan computer wanda ake amfani da su wajen aikawa da ita kanta computer sako, wato ana yin amfani da su irin wannan bangare na Hardware wajen aikawa da computer abu daga waje zuwa cikin ta. Kadan daga cikin Input Devices Hardware sun hada da:-

Duk inda ka ji an ce Input Devices ana nufin kayan computer wanda ake amfani da su wajen aikawa da ita kanta computer sako, wato ana yin amfani da su irin wannan bangare na Hardware wajen aikawa da computer abu daga waje zuwa cikin ta. Kadan daga cikin Input Devices Hardware sun hada da:-

Computer Keyboard ke nan wanda yake da maballai 102

Keyboard: shi Keyboard wani shinfidadden allo ne mai wasu maballai ajikin shi, ana amfani da shi wajen yin magana da computer ko kuma aika mata da sakon rubutu, wanda rubutun ya shafi lambobi da haruffa da bakake da kuma alamomin rubutu, kamar su alamar motsin rai, da alamar tsayawa ko kuma alamar tambaya, sannan kuma ajikin wannan Keyboard akwai wadansu karin maballai wadanda ake kiran su da (Functions Keys) wanda suke yin aiki daidai da yadda wanda ya tsara wani program yake son suyi aiki. Saboda haka, shi Keyboard shine babban Input Device Hardware da ake da shi wanda da sh ine ake iya magana da computer ta rubuce. Idan muka dubi tsarin Keyboard da ake saka shi a jikin computer ta gida ko kuma muce Desktop Computer za mu fahimci cewar muna da Keyboard launi biyu. Akwai Keyboard da yake da maballai 101 sannan akwai Keyboard da yake da maballai 105. Amma Keyboard da ake samu a wasu kananan computer irin su laptop su ba yawan maballansu daya da na Desktop Computer ba. Cikakken bayani akan Keyboard da yadda aka karkasu zai zo nan gaba.

Daya daga cikin Mouse da ake da su a computer

Mouse: wannan a hausance za mu iya kiranshi da (dan bera) domin yadda aka yi shi da igiya a jikin shi wacce ta hada shi da computer sannan kuma aikin da yake yi shine, yana zama a mazaunin hannu a wurin mutum, wato, idan ka rike Mouse da hannunka idan ka duba jikin Monitor din ka za ka ga wata ‘yar kibiya, idan ka matsar da Mouse za ka ga wannan kibiyar tana matsawa. Shi yasa Mouse yake zama a mazaunin hannu a wajen computer, duk abinda kake son ka dauka ko kuma ka taba a cikin ita computer, to, za ka yi amfani da Mouse ne wajen dauka. Ko da yake shi Mouse ya na cikin jerin kayayyakin computer wanda ake rike su da hannu kuma ake nuna computer da su (Pointing devices), to amma kafin lokacin da za mu warware bayanai akan su, ya kama ta mu sani cewar Mouse yana da maballai guda biyu, wanda su ne suke taimakawa mai amfani da shi wajen sarrafa abu a cikin computer, yana da maballin hagu (left click) wanda yake mazaunin, taba, dauka, ajiya da dai makamantan su. Sannan kuma a maballin dama (right click) wanda yake mazauni mai baka bayani akan abinda ka taba. Cikakken bayani game da Mouse da karkasuwarshi zai zo nan gaba.

daya daga cikin Computer Microsphone

Microphone: wacce a hausance muke kira da makirfon ana hada wa computer Microphone kuma yana mazaunin kaya da ake amfani da shi wajen shigarwa da computer sauti ko kuma yin amfani da sauti wajen baiwa computer umarni. Idan zamu tuna lallai makirfon a masallatan mu suna taimakawa  wajen isar da sako ga wadanda suke a nesa, su ji abinda ake fadi, kuma ai muna yin amfani da makirfon mu dauki karatuka a jikin rediyo ko kuma video ko kuma mu yi amfani da makirfon mu yi magana a jikin rediyo a mazaunin amfilifaya. To dukkanin irin wadannan abubuwa da ka ke iya yi da Microphone zaka iya yinsu da shi a jikin computer. Ita kuma Microphone da ka hada shi da computer zama ka iya ba ta umarni, irin  na kunnawa da kashewa, za ka iya amfani da shi wajen bude wani program a computer da dai makamantansu.

Daya daga cikin PC Camera da ake amfani da su wajen daukar hoto, ko kuma Video Call

PC Camera: shi PC Camera yana daga cikin fitattun kayan da ake amfani dasu wajen sakawa  computer abu a cikin ta, sai dai shi PC Camera, wato Camera ce da ake hada ta da computer domin a dauki hoto a saka a cikin computer, ko kuma a dauki hotuna masu motsi (Motion Picture) a ajiye su a cikin computer.  Camerar computer ba daya take da camera wacce muka saba aiki da ita na yau da kullum bace, ita tana aiki ne kawai a computer ba za tayi aiki ba idan ba a hada ta da computer ba. Duk da cewar a wannan lokaci akwai wadansu camerori da ake hadasu da computer kuma suyi aiki kamar PC Camera sannan kuma ayi aiki da su kamar yadda ake aikin yau da kullum. Cikakken bayanai akan Camera da karkasuwar su zai zo nan gaba.

Scanner ke nan wacce ake yin amfani da ita wajen sakawa computer hoto a cikin ta

Scanner: ita ma tana daga cikin shahararrun Input Devices da ake amfani da su yau da kullum, amma kuma aikin ta shine ya mayar maka da abunda yake a kasa ya koma cikin computer, misali kamar kana son ka yi aiki da hoto amma kuma hoton baya cikin computer za ka yi amfani da scanner ka saka wannan hoto a cikin ta ita Scanner ita kuma Scanner ta mayar maka da shi cikin computer, haka zaka iya daukar rubutu da yake cikin littafin ka saka shi cikin Scanner ita kuma ta mayar maka da shi cikin computer. Dukkan abinda yake cikin computer kamar rubutu, wasiku da kamar su hotuna ana kiransu da (Soft copy) abunda aka fitar da shi a jikin takarda wanda ya hada da hotuna da rubutu shi ake kira da (Hard copy). Sabo da haka ita scanner tana taimaka maka wajen shigar da Hard Copy na abu ya koma Soft Copy. Ita kanta scanner ta kasu kashi – kashi wanda bayanan su zai zo a nan gaba.

Wadannan suna kusan shahararrun Input Devices da aka saba yin aiki da su yau da kullum, ko da yake akwai sauran Input Devices Hardware da  ba mu yi magana akan su ba wanda nan gaba zamu tattauna suma akan su.

Me ake nufi da abin fitarwa (output devices)?

Su kuwa Output Devices Hardware su kaya ne na computer da ake amfani dasu wajen fito da sakamakon abinda Input Devices suka shigar. Fitattun Output Devices sun hada da:-

Deskjet Printer ke nan wacce ake amfani da ita domin fitar da rubutu mai launi a cikin computer

Printer: shine wanda zamu iya kiran shi da mababa’a wato ita Printer ana amfani da ita ne a fitar da rubutu da kuma zane zane da aka yi cikin computer zuwa takarda, kusan ko wane mai aiki da computer yana bukatar Printer domin idan ya gama shirya takardunshi ya fitar da su, shi yasa Printer ita kuma ta canji scanner, domin kamar yadda muka yi bayani a baya Scanner tana mayar da abu da yake Hard Copy zuwa Soft Copy, to ita kuma Printer tana fitar da Soft Copy ya zama Hard Copy. Kusan akwai Printer iri iri da ake da su wadanda kuma suka sha banban wajen aiki. Akwai Printer da take iya fitar da takarda da bakin tawada ne kawai (Black ink) sannan kuma akwai wacce take iya fitar da takarda da baki da kuma launi na tawada (Colour ink). Sannan kuma ta bangaren masu fitar da launi na tawada akwai wadanda suke da tawada mai hoda sannan kuma akwai masu tawada mai ruwa. Cikakken bayanai akan yadda Printer take da kuma karkasuwar ta zai zo nan gaba.

LCD Monitor daya daga cikin Computer Monitor da ake da su

Monitor: shine wannan abu mai kama da talabijin da kake gani gaban masu amfani da computer. Ita Monitor kwarai da gaske TV ce amma kuma ba TV bace irin ta gida, domin ita ana hada ta da gidan computer ne domin ta fitar da abinda mutum ya ke yi a computer, misali da babu shi Monitor, to da ai ba za ka san abinda ke faruwa ba a cikin computer na program da ake aiki da su ba, misalin rubutu da ake yi a cikin computer. Shi yasa suka kira shi da Monitor mai lura da abun da yake gudana a cikin computer. Shima Monitor ya karkasu kamar yadda sauran suka kasu. Misali idan kai ma’abocin zuwa wurare irin su banki, ko ma’aikatu za ka ga a wasu wurare suna da Monitor mai kamar TV mai doro wacce ake kiran ta da CRT (Crystal Ray Tube) wannan kusan ada zaka same ta a ko’ina saboda itace aka fara kirkira, tayi kama da TV matuka. Sannan kuma akwai Monitor wanda ake kira da LCD (Liquid Crystal Display) wanda yake a yanzu zaka gan shi yayi kama da Plasma TV wato irin TV’n nan da ake dorata a jikin bango. Sannan kuma cikin su irin wadannan Monitor akwai wacce take da jan wuta akwai wacce bata da jan wuta, akwai wacce take da cin idanu (Radiation) akwai kuma wacce bata da cin idanu. Gamsasshen bayani akan karkasuwar Monitor da yadda su ke yin aiki zai zo nan gaba.

Speaker ke nan da ake amfani da ita wajen jin sauti daga cikin computer

Speaker: shima daya ne daga cikin Output Devices Hardware da ake dasu, sai dai shi Speaker yana taimakawa ne wajen fitar da sauti daga computer wato, duk irin karatun da za ka saka cikin computer ko kuma sauti zaka iya jinsu ne kawai idan kana da Speaker a jikin computer ka. Ko da yake ita Speaker a jikin computer ba ta da wasu darajoji na musamman kamar yadda wasu daga cikin kayan computer suke da shi, sai dai kamar yadda ka sani iya kudinka iya shagalinka, iya girman Speaker da ka saka wa computer ka iya kara da sauti da za ta iya fitar maka da shi.

Wadannan sune kadan daga cikin shahararrun Output Devices Hardware da ake da su, duk da yake akwai wadansu Output Devices da ake dasu wadanda zamu yi bayanan su a fitowar mujalla ta gaba.

Me ake nufi da Communication Devices? Abin Sadarwa

Su kuma Communication Devices Hardware su kayayyaki ne da ake amfani da su tare da da computer wajen harhada computoci ta hanyar musayan umarni, wato su Communication Devices  sune ake amfani dasu idan ana son a aika da sako daga wannan computer zuwa wata computer, abubuwan da ake iya sadarwa sun hada da rubuce-rubuce, da irin su hotuna da video da dai makamantansu. Su Communication Devices sun hada da:-

Wannan shine Ethernet Modem da ake amfani da shi ta hanyar sadarwa tsakanin computer da wata computer

Modem: yana daya daga cikin Communication Device da ake amfani dasu wajen sadarwa ko kuma hada wata computer da wata ta hanyar amfani da shi a hada shi da ita computer a ramin da yayi kama da rami wayar tangaraho da ka sani, ko da yake su modem sun karkasu kashi kashi kuma suna da dangi iri iri da kuma karfi da  kuzari wajen tafiyar da sako daban-daban. Misali akwai modem da yake a jikin computer wato yana hade da Motherboard din ta wanda ake kira da (internal), sannan kuma akwai wanda yake wajen computer wanda ake kira da (external). Ko da yake akwai wadansu irin abubuwa da ake amfani dasu wajen hada sadarwa da computer wanda a zahiri su ba Modem bane amma wani dalili sai yasa su zama Modem, wannan kuwa ya hada da wayar tafi da gidan ka (GSM) wanda cikakken bayani game da shi zai zo nan gaba.

Bluetooth: kamar yadda kowa ya sani cewar ana amfani da Bluetooth wajen aikawa da sako daga wannan waya zuwa wannna waya, to itama computer da take da Bluetooth za ta iya aikawa da sako zuwa waninta wacce take da Bluetooth. Cikakken bayani game da yadda Bluetooth yake yin aiki yana nan tafe.

Infrared: shi ma infrared kamar yadda masu amfani da wayoyi suka sani ana amfani da shi wajen aikawa da sako daga wannan waya zuwa wata wayar, to haka computer da take da infrared zata iya aikawa da sako ga wata computer mai infrared duk da cewar sakon da zaka iya aikawa ta infrared bai daukan dogon zango kamar yadda wadancan abubuwa na baya da muka yi bayani a kan su.

Wadannan suma sune mafi shahara daga cikin Communication Devices  da muke da su wanda akwai wasunsu, wanda suke da amfani matuka da kuma taka mahimmiyar rawa wajen aikawa da sako a cikin ita computer.

Storage Devices Abin ajiya, me ake nufi da abin ajiya?

Abin ajiya wato Storage Devices su ne kayayyakin da ake yin amfani da su wajen ajiyar Data ko Information domin amfanin gaba, wato sune suke taimakawa computer wajen ta iya ajiyar kaya da kuma dukkanin bayanai da suka kunshi program da hotuna da rubuce-rubuce da dai makamantansu, domin idan ka zo gobe ko nan gaba zaka same su a kintse. Suma kadan daga cikin irin wadannan kaya da ake amfani dasu wajen ajiyar Data ko Information suna da dan dama wanda suka hada da:-

Floppy Disk a saman Floppy Drive wanda ake iya jiyar abubuwan computer a cikin su

Floppy Disk: ko kuma kirashi da Diskette shi wani mazubi ne wanda aka yi shi domin ya rinka daukan kanan program wanda girman abinda yake iya dauka bai wuce 1.44mb (Mega Byte). Da yake a wannan zamani da muke ciki yana da wahala ka samu wani wanda yake amfani da computer yana amfani da Diskette, kasancewar a yanzu akwai wadansu abubuwan ajiya wadanda suka fishi ajiyar abu mai yawa da nauyi, duk da cewar Diskette ya taka mahimmiyar rawa a lokacin da aka fito da shi a wancan lokacin domin ya fara bayyana ne tun cikin 1970’s. Ko da yake kamfanin da suke fito da shi (IBM) sun fara fito da wanda yake da fadin inchi 8, daga bisani suka rage shi ya koma inchi 5.25 a wajen fadi. Amma mu Diskette din da muka tarar wato lokacin da computer ta shahara a shaguna da makarantu a Africa mun sami Diskette ne wanda yake da fadin inchi 3.5, cikakken bayani game da yadda Diskette yake yin aiki ya nan tafe.

Zip Drive wanda ake iya ajiyar abubuwa masu nauyi a cikin sa

Zip: shi Zip yafi Diskette daukan kayan computer, domin shi yana daukan kayan computer daga 100MB ko kuma fiye da haka. Ko da yake su jerin irin wadannan Disk din ana saka su a cikin jerin High Capacity Floppy Disk, sabo da irin abubuwa masu nauyi da ake iya saka musu wanda sai ka sani asalin karamin Diskette guda 69 su iya daukan abinda karamin Zip Disk guda ke iya dauka. Ko da yake su kansu wadannan High Capacity Diskette suna da jerin dangogi iri-iri da kuma nau’o’i daban-daban, daga ciki akwai wadanda ake kiransu da SuperDisk wanda ake iya ajiyar abu daga nauyin 120MB zuwa abinda yakai 200MB. Har ila yau akwai wani da ake kiran shi da Zip Drive wanda fadinshi kamar fadin Diskette ne wato inchi 3.5 wanda yake da  sauri wajen bincikan abinda aka ajiye mishi ko kuma saurin aji ya, wanda yake farawa daga 250MB kusan abinda Diskette 173 za su iya kwashe wa. Sabo da haka mafi ya yawancin computoci a wancan lokacin sukan zo da gidan da ake zira shi Zip Drive wanda zaka iya saka manyan hotuna masu motsi (Video) da sauti masu girma, da kuma manyan ayyuka wanda ba ko wane ma’ajiya bace zata iya ajiya ko kuma kwashewa.

Hard Disk wanda aka fi sani da kwakwalwar computer shine yake ajiyar abubuwa masu matukar mahimmanci da kuma nauyi

Hard Disks: shine makunshi mai girma wanda ake sa ran yafi kowane irin mazubi da yake jikin computer wajen adanar kaya ko kuma bayanai. Amma da farkon fari, lokacin da aka shigo da irin wadannan computer da muke ganin su a cikin gidajenmu da makarantun mu da ofisoshin mu, a wancan lokacin program da ake saka wa computer basu da girma, a sanadiyyar rashin girmansu ya zamanto su wadancan computocin basu da Hard Disk. Ilimi na kara zurfi bukatar da ake da ita na computer tana kara fadada kuma program da ake saka wa computer sai ya zamanto sun fi karfin su zauna jikin Diskette, saboda wannan dalili ne yasa kamfanoni da suke kirkiran kayan computer suka kirkiro Hard Disk. Hard Disk wanda kowace computer a yanzu take da shi yana da girma matuka wajen ajiyar kaya ko bayanai ko kuma sauti, ga ta da kuma tsananin sauri fiye da Zip ko Diskette, shi yasa Hard Disk yake zama shine babban mazubin ajiya da shi kanshi kundin computer da ma dukkanin wasu program da suke cikin computer suke zaune, wanda karancin Hard Disk yana farawa ne daga 4GB (Giga Byte) zuwa Illa masha Allah. Cikakken bayanai game da yadda Hard Disk yake da yadda yake yin aiki yana nan a tafe da izinin Allah.

CD ROM ko DVD ROM sune ake yin amfani da su wajen ajiyar abubuwa a cikin faifai na disk

CD/DVD: su kuma kamar yadda muka sani CD shine dai irin CD’n da ka sani ake amfani da shi a Video ko kuma rediyo irin taka ta gida, haka DVD shima ka zalika. Amma da farko a da kamar yadda muka fada a baya cewar computoci suna zuwa babu Hard Disk a kansu saboda rashin nauyin program, haka a da idan ka sayi computer za ta zo ne da Diskette dauke da mafi yawa daga cikin program din ka da kake son kayi amfani da su. To, zamani na tafiya abubuwa suna kara karuwa sai ya kasance cewar duk wani program da kake son ka saka a cikin computer yafi karfin  Diskette sai dai a saka shi a cikin CD wani lokaci ma yafi karfin CD sai dai a saka shi a DVD. Domin shi CD yana da girma ko kuma nauyi kayan da yake iya dauka ba sa wuce 700Mb shi kuwa DVD da muka fi sani yana farawa ne daga 4.7Gb wanda yake kwatankwacin CD guda bakwai (7) ke nan. Duk da cewar akwai banbaci da kuma ire iren irin wadannan kayan ajiya da ake da su, ta bangaren CD da DVD suna cikakken bayanan su ya nan tafi.

Tapes: kaset mai kama da kaset na radiyo shi wannan kaset ana amfani da shi wajen ajiyar data ko kuma information a cikin computer, ko da yake yana yin tsarinshi ya sha banban da na karamar rediyo, shi wannan Tapes wanda ake iya sarrafashi kamar yadda kasan ana sarrafa kaset na rediyo, kamar matsar da shi gaba, dawo da shi baya da dai makamantansu. Sannan kuma shi wannan tape suna da nau’o’i daban-badan a misali mafi kankantar tapes na computer yana farawa daga karfin aji na 40Mb zuwa 5GB wanda ake kiranshi da Quarter Inchi Cartrage, sannan kuma akwai wanda yake farawa daga 2GB zuwa 24GB wanda ake kira da Digital Audio Tape. Sannan kuma akwai wanda yake farawa daga 20GB zuwa 40Gb wanda ake kiranshi da Digital Linear Tape. To mene ne banbanci tsakanin su, zamu ji ci kakken bayani a nan gaba.

A takaice wadannan sune kadan daga cikin shahararrun ma’ajiya da ake dasu, wadanda ko wannen su ana iya zuba data ko information na computer kuma a same shi a gaba. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, akwai wadansu abubuwa da muka saba fadinsu a sakamakon yawan amfani da waya wanda a zahiri yadda mutane suke fadansu haka ne, amma idan suka shigo ga ilimin computer za ka tarar ba haka bane, kadan daga ciki shine Memory, mutane suna amfani da wannan kalma idan suna son su ajiye abu a cikin waya ko kuma su baka labari game da ita. Misali “memory na wayata 1GB”, to shi memory a computer ya sabawa memory da muke fada a waya, shi memory a computer ba waje ne da ake ajiyar abu na din-din-din ba, wuri ne da ake a jiyar abu na wucin gadi. Domin sanin mene ne cikakken banbanci tsakanin Storage devices da kuma Memory na computer mu hadu a bugun mujalla na ga, wanda zamu tashi a darasin Gidan Computer (System Unit).

23 COMMENTS

 1. Gaskiya kam kuniyi kokari dan kun kara mana haske a fannin comuter amma sai dai banga types da important din computer ba

 2. kai wannan shafi da kuka kirkiro yana da matukar amfani ga yan uwan mu hausawa, ina rokon Allah ya kara maku fahimta ta yanda duk mai karatun computer zai amfana dasu, mun gode Allah ya kara maku jagora

 3. Allah ya saka muku da alkairi. Sai dai naga akwai wani akwati da ake jona masa wayoyi kusa da monitor ban ga ka fade shi ba da kuma amfaninsa. Da fatan za’a turon karin bayani via email Allah ya taimaka ya kara basira.

  • Wannan haka yake shine karatu naga da muka ce zamu yi idan mujallar ta fito, kamar yadda muka fadi a karshen ita wannan takarda.

 4. hakika babuwani wani abinfada ko cewa saidai fatan ALLAH yasakamuku da alkhairi,yakukara lafiya da kwaringuywa,yataimaka muku damu dalibai ALLAH yabamu ikon fahimta da azaka amin.

 5. dan allah kuna koyar da karatun computer acikin harshen hausa kuma idan kuna ko yarwa a ina kuke koyarwa kuma menene tsare tsaren ku nagoda allah yakara basira

 6. slm gasikya abinda zanfara cemaku allah yasaka muku da alheri.muna masu alfahari daku saboda gudunmawar dakuke bawa hausawa daharshen hausa…

 7. Slm malan!!Agaskiya nayaba da yanba naga tsarin koyarwar ALLAH yasaka da alheri.Abinda nakeso nasani shine kamar. Kwana nawane “asati” za’azauna, sannan kuma yushene za’a fara “regisreton”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here