MATSALAR SHANYEWAR BATIRIN WAYA DA HANYOYIN MAGANCE SU

Matsalar zukewar batirin waya da sauri, kin yin cajin batirin cikin hanzari da makalewar manhajoji lokacin son yin amfani da su, kadan ne daga matsalolin da suke addabar masu amfani  da wayar Android. Amma In Sha Allahu zamu taimaka wurin kawo manyan dalilai da suke kawo wadannan matsalolin da kuma hanyar magance su.

Tsayar da Manhaja

Abu na farko shine sanin wadansu manhajoji ne suke shanye batir da wuri, sannan mene ne amfanin su a lokacin da suke yin aiki. Domin a wani lokaci mutum zai iya kunnan application a wayarsa kuma bai rufe su ba sannan ya sake bude wadansu. To barin app a kunne suna aiki a karkashin kasa, na daga cikin abubuwan da suke zuke batiri da sauri.

Amma domin sanin wadansu manhajoji ne suke yin aiki a karkashin kasa kuma ya yanayin jan batiri da suke yi, mutum na bukatar ya shiga settings>Battery. Wannan zai sa kaga wadansu manhajoji ne suka fi zukar cajin batir da kuma shin wadanda kake son yin amfani da su, su ne ko kuma wanda dole wayar tana da bukatar su domin ta yi aiki ne?

Idan manhajojin wayar ce ke butakarsu to dole ka yi hakuri ka barsu su ci gaba da aikin su, domin hana su aiki zai kawo matsala ga aikin da ita wayar take yi. Amma idan manhajoji ne wadanda suke taimaka maka wurin yin aiki to sai ka danna force stop.

Akwai manhajoji masu dinbin yawa a Play Store wadanda suke taimakawa wurin sanin hakikanin mai yake faruwa da batirin wayar mutum. Mu a nan zamu iya ba da shawarar saukar da GSAM Battery Monitor. Idan ka saukar da wannan manhajar, zai iya daukan kwanaki yana binciken lafiyar batirin wayar da kuma abubuwan da suke zukarsa. Bayan ya kammala zai baka cikakken rahoto dangane da batirin.

Canza sabon Batir

Wani lokaci zaka iya samu cewa wayar da mutum ke amfani da ita tsohuwa ce. Misali kamar yadda da yawa daga cikinmu suke siyan wayar hannu wacce wani yayi amfani da ita, ko kuma amfani da yawa da aka shigo da su daga wasu kasashe amma kuma ba sababbi ba. To gaskiyar magana shi ne, idan har ka duba cewa babu irin wadancan manhajoji masu aiki a karkashin kasa masu zuke batir, kuma ka rage hasken fuskan wayar, to magana ta gaskiya shi ne ana bukatar sabon batir a wannan wayar.

Kamfanonin da suke yin batirin waya sun ce ana iya yin cikakken cajin waya har sau dubu daya (1000) kafin ya fara saurin zukewa, amma shima hakan ya danganci wani kamfanin ne yayi batir din.

Idan ka yi dace wayar ana iya cire batir din ta, to babu matsala sai a cire batir din a canza shi da sabo, amma kuma idan irin wayoyin da ba a cire batir din su ne, to yana da kyau ka kaiwa kwararru ko ma kamayar da wayar zuwa ga kamfanin da suka kera ta idan a garin da kake akwai su, su cire maka batir din su mayar da sabo.

A wurin canjin batir akwai korafi da jama’a suke yi musamman idan suka sa sabon batir sai su ce shima sabon baya dadewa, ko kuma yana dadewa bai yi caji ba. To akwai matsaloli guda biyu ga hakan. Matsala ta farko shine ba a duba karfin batirin da wayar take bukata ba. Domin bakin da ake zura batir yayi daidai da naka amma kuma karfin da wayar take take bukata bai kai ba, matsala ce, kuma idan batir din bai kai karfin da wayar ke bukata ba zai yi saurin zuke batir din.

Cajar Wayar bata aiki yadda ya dace

Matsala ta biyu kin yin caji da sauri, shima yana da alaka da sabon batirin da ka saka, misali ka saka batirin da yake da 1000mAh kuma sai ka sami cajar wayar da take sa karfin 300mAh to yana nuna maka cewar sai kayi jira har sau uku kafin ta cika. Wadannan matsalar abin lura ce kuma haka ake magance su.

Shi yasa yake da kyau sosai duk lokacin da mutum ya ke son sayan caja to ya tabbatar ya sayi ta kamfanin wayarsa. Wani lokaci amfani da caja mai karfin da tafi na batiri shima matsala ne, domin zai yi saurin kona sinadaran da suke ajiyar caji da wuri, kuma gasa batirin da sauri zai iya lalata shi ba da jimawa ba, kuma wani lokaci koda ka samo cajar asali da aka yi domin wayar sai ka ga bata iya yin komai a wayar.

Android System yana amfani da batir sosai

Daya daga cikin abin daya fi komai zukar batir shi ne Android System. Android System shine babbar manhajar da take taimakawa wayar domin ta yi aiki kamar yadda ya kamata, tsayar da ita tamkar tsayar da wayar ne ko kuma lalata ta.

Ga ka’ida na wadanda suke yin OS na Android sun ce Android System bai kamata ya wuce kashi ashirin da biyar cikin dari (25%) na batirin wayar ba. To amma idan aka samu ya wuce haka, to ya nuna cewa akwai matsala sosai, kuma babu wata hanya da za a iya magance wannan sai ta hanyar ragewa wayar babbar manhajar da ita kanta wayar take amfani da ita.

Misali ace wayar tana amfani da nadroid Lollipop ne sai ka dawo da ita zuwa Android Kit-kat. Akwai hanyoyi da dama da ake amfani da su wurin ragewa OS an Android daraja da ake samu a shafukan intanet, kawai ka rubuta downgrade (sunan wayarka). Yin hakan shi ne kawai mafita, amma mu sani hakan kuma na matsayin kayiwa wayar flashin ne, amma wani abun jin dadi koda lokacin da kake kokarin rage mata daraja an sami matsala zaka iya yin factory reset, wayar zata dawo daidai.

Google Play Services yana zuke batir

Google Play Services shima yana daga cikin abubuwan da suke zuke batir da wuri, abin haushi shine ba zai yiwu ka tsayar da shi ba, domin shi ke taimakawa wurin ganin manhajojin da suke cikin wayar suna da alaka tsakaninsu da wanin su, musamman ta wurin musayar bayanai. Amma duk da haka akwai yadda zaka iya rage wannan cajin.

Je Settings>Applications>All>Google Play Services sai ka taba maballin Clear cache. Wannan zai goge duk wani abubuwa da wannan manhajar ta ke tattare da su sannan ta fara gina wadansu, wanda wannan zai rage shan batir, zaka iya sake yin haka kowane wata.

Kashe Auto-Brightness

Dangane da matsalar hasken fuskar waya, kusan da yawa daga cikin mu mun fi barin cewar wayar mu ta rinka lura da haske da kanta wato auto brightness. Barin wayar ta rika lura da shi da kanta ba shi ke nuna hakan daidai bane.

Matsalar a nan ita ce, censor da yake jikin wayar yana aiki tukuru wurin sanin wani wuri ita wayar take, shin akwai haske mai yawa ko kuma babu, idan akwai haske to sai fuskar wayar yayi duhu, idan kuma akwai dubu a wurin sai ta yi haske, saboda haka barin sa a auto yana taimakawa wurin ganin cin batir.

Yadda idanun mu suke bukatar haske ya sha banban da na kowa, saboda haka yana da kyau ka tsayar da wayar ka zuwa hasken da ka san shi ya fi dace da kai, kuma hakan zai taimaka wurin ganin batirin baya karewa da wuri.

Rage dadewar disashewar hasken waya

Kamar yadda muka sani hasken da ke fita ta fuskan waya na daya daga cikin abubuwan da suke zuke batir musamman wayoyin Android. Saboda haka lura da tsawon lokacin da wayar take yi cikin haske sosai yana da amfani.

Lura da tsawon lokacin yana da matukar muhimmanci domin a wani lokaci wasu sukan bar hasken ya kai kusan minti biyar ko goma kafin yawar ta disashe haskenta ko kuma ma ta tafi barci. To kamar dai yadda na fada dadewar hasken fuskar wayar yanayin zukar batir.

Yana da kyau mu rage daga dogon lokaci zuwa gajere, misali daga minti guda zuwa dakikoki ishirin ko kasa da haka. Hakan zai taimaka wurin kara rage cinyewar batirin waya.

Lura da ‘yan kanzagin app (widgets) da masu aiki karkashin kasa

Wadannan manhajoji da akek kira da Widgets su wakilan manhajoji ne da suke tsayawa a fuskar wayar mutum suna sanar da shi wadansu al’amura da asalin manhajar take yi. Misali manhajar duba yanayi, wato Weather App, manhaja ce mai zaman kanta amma kuma wadanda suke yinta sai su yi mata dan kanzagi (widgets) wanda zai wakilci shi babban da bai bukatar kodawane lokaci sai an budeshi za aga abin da ke ciki.

To irin wadannan manhajoji kasancewar akwai guda daya ko biyu nasan mutum ba zai damu ba, amma yana da kyau mu sani cewar irin wadannan manhajoji suna aiki ne a karkashin kasa domin aiwatar da ayyukansu. To idan mutum yana da su da yawa a cikin wayarsa to ya sani haka saurin shanyewar batiri zata kara kazanta.

Saboda haka, irin wadannan manhajoji irin na labarai masu neman shiga intanet da yin aiki ta karkashin kasa yana da kyau. Haka irin manhajojin da suke bukatar yin update kodawane lokaci suma suna da matsalar cin batiri wani lokaci yana da kyau mutum ya tsayar yin automatic update na waya ya sa shi zuwa wani ayyanennen lokaci kamar sau daya a wata. Shima hakan zai taimaka wurin rage ci batiri.

Wannan shi ne dan kadan daga wasu abubuwa wanda muka ga suna daga cikin musabbabin cinye karfin wutar batiri, kana da wata matsala? Mu tattaunata a wannan wuri!

12 COMMENTS

  1. Comment: Hakika muna alfahari da wannan bawan ALLAH da ke fashin baki ko karin bayani akan na’ura mai kwakwalwa ALLAH ya saka maka da Alkairi.

  2. Assalamu Alaikum

    Malam Salis computer nane ta fadi screen nata yayi ruwa ruwa.

    Shin zai iya gyaruwa ko sai dai a canza..??

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here