Hattara Dai Akwai Barayi A Internet Da Wayar Hannu!

Rubutawa: Salaha Wada Wali

Sanin kowa ne zuwan computer da waya sun fito da sabbin tsare-tsare waɗanda suka jiɓanci ƁARAYI da salon sata kala-kala, ta hanyar amfani da computer ko waya.

DAMFARA A INTERNET

Ana samun mutane masu amfani da damar su da asirinsu wajen jawo hankalin mai mu’amala da internet wajen sa kayan bogi ta hanyar jiran ko ta kwana, da nuna alamun sani a gare ka, amma kuma babu sanayya, yana da kyau mu yi amfani da basirar da Allah ya baka, wajen ƙoƙarin gano ya abin yake kafin ka faɗa hannunsu kamar dai yadda Bahaushe yake cewa: “IDAN MUTUM YACE ZAI BAKA RIGA, TO KA DUBA TA WUYANSA” wannan ƙarin magana Ya ƙarawa Hausawa basira da dogon tunani wajen sanin mai baka.

KIRAN WAYA

Wani ya kan kira wani da nuna alamun zai gabatar da kansa harma ya canza wa layinsa code da cewar yana Turai, sukan bi wurare daban- daban wajen sace wa mutane wayoyi da computer.

 INA MAFITA GA ƁARAYI?

  • Ya kamata ka katse wayarka idan mutum ya kiraka, kuma baka fahimci abin da yake nufi ba, ko kuma ka kashe wayarka tsawon minti 10 ko 30, sakamakon sauraronsa zai sa a ci galabar ka, tun da suna da magani da dabara wajen ƙwarewar aiki.
  • Ga me Nokia akwai wasu applications da aka tanadar don magance matsalar hakan. Ka ziyarci OVISTORE don samunsa ko kuma ɗauko Antivirus game Symbian ka shiga Anti lost ka sa lambar wani wanda idan wayarka ta ɓata ko an sa ce, ana sa wani la yin zata turo map na wurin da wayar take.
  • Masu Samsung, LG, motorola, Siemen, Philips, da sauransu sai ka shiga setin na wayarka sannan Security ka sa lambar wayar wani naka wanda da zarar wayarka ta ɓata ana canza la yi zata turo lambar la yin da aka sa zuwa lambar ɗan uwanka, sai ka kira don samun wurin da wayarka take, yana yi har kan China phone. Ko kuma ziyartar shafukan wayankaɗan samun mafita.
  • Yi amfani da serial number na wayarka wajen kulle wayar idan an ɗauke ta. Danna *#06# sannan ka kira kamfanin la yinka da wata wayar ka ba su lambar IMEI za su tura ta zua 3GPP su ne suke da alhakin kulle wayarka.

KIRA GA MASU UNLOCK

Yana da kyau ku yi amfani da basirar ku wajen gano mai waya idan an kawo muka unlock, domin kalar mutum kalar wayarsa.

BAR AMSA

Yi sharhin ka
Shigar da suna a nan