Hanyoyi biyar (5) da ake bi a gane inda wayar “Android” take bayan ta bace ko an sa ce!

Rubutawa: Tukur Kwaironga

Dukkanin wani abu da ya kasance ƙarami ba shi da wahalar a ce an ɗauke shi ko kuma ya faɗi. Ƙananan wayoyi na hannu suna da daɗin sha’ani da kuma sauƙin amfani, wasu suna da sauƙi ko arha a wajen siya, wasu kam ɗan karan tsada ke gare su, wanda ya zamanto sai ka jajirce ka daure za ka iya sayensu.

Mafi yawancin masu riƙe da wayoyin hannu suna ƙoƙarin kaffa-kaffa da su saboda masu farautarsu. Da wannan dalili ne ya sanya muka zaƙulo muku waɗannan hanyoyi guda biyar (5) da za su taimaka wa wanda yake da waya mai tsarin Android idan ta ɓace ko an ɗauke ya iya gano inda take.

1.            Contact Owner: (https://sites.google.com/site/paranoidandroidproject/ContactOwner)  wannan wani ɗan karamin application da ake samun shi a Android Market wanda yake taimaka maka wajen rubuta bayanai game da kanka wanda idan mutum ya tsinci wayarka zai ga cikakken sunanka da adireshinka, wanda hakan zai taimaka wajen neman ka idan wayan ta faɗa hannun nagari ne. Hanyar da ake amfani da wannan ɗan application hanya ce mai sauƙi wacce da zarar ka saukar da shi wannan application a cike shi ne sau ɗaya, za ka iya yin amfani da bayanai naka da ke cikin wayarka, ko kuma ka rubuta su kai tsaye. To, duk sadda ita wayar taka ta je dan hutu zata kulle kanta sai waɗannan bayanai da ka saka su bayyana a jikin fuskarta.

2. Wheres My Droid.      (https://market.android.com/details?id=com.alienmanfc6.wheresmyandroidwannan ) Wannan application yana da matuƙar amfani wanda shi ma zai taimaka maka wajen gano inda wayarka ta hanyar amfani da “GPS”. Shi wannan application yana iya baka dama ka kunna Ringtone ɗin wayarka ko kuma ka kashe Ringtone ta hanyar aikawa da Text Message daga wata wayar, kuma idan wayar ɗauke ta aka yi wannan application zai taimaka maka wajen hana barawon yin waɗansu muhimman canje-canjen.

3.            Anti-Virus Software: za ka iya yin amfani da waɗansu shahararrun Anti-Virus software domin gano inda wajen inda wayarka take. Misali AVG Anti-Virus na waya idan ka saka shi a cikin wayar yana zuwa da dan wani karamin application mai suna Lost-Phone-Tracking. Idan ka saka Anti-Virus na AVG sannan ka yi “configuration” na shi wannan application nasu, su kamfanin za su taimaka maka wajen kulle wayar taka sannan ka iya gano wayar ta hanyar amfani da google map. Sannan akwai wani application mai suna Lookout Security & Antivirus shi ma kusan yana irin wannan aiki wanda suke iya baka damar idan waya ta ɓace ka iya gano ta ta hanyar Internet.

4.            Kamfanonin SIM: wasu daga cikin kamfanonin da suke bada service na waya kamar T-Mobile, da irin su Verizon dukkansu suna da application na musamman da suka yi domin gano wurin da wayarka take idan ta ɗace.

Plan B: To idan duk waɗannan hanyoyi guda huɗu sun ki yin aiki, to, ga wata sabuwar hanya mai suna “Plan B” wanda ko da baka samu damar saka wani application da ke bada damar gano wayar ka ba, to wannan application ɗin zai iya gano maka wayarka ta hanyar turo maka da saƙon SMS da kuma taswirar wurin da wayar take zuwa ga akwatin gmail naka.

Duniyar Computer
Salisu Hassan wanda aka fi sani da Salisu Webmaster shine shugaban wannan Muhajja ta Duniyar Computer kuma shugaban kamfanin Duniyar Computer, yana da kwarewa a fannoni da dama na Computer, ya kirkiri shafuka da manhajoji na computer da waya masu yawa, yana da kwarewa a fanni addinin Musulunci, yana jin Turanci da Hausa da Larabci. Magidanci ne kuma yana zaune a garin Kaduna a halin yanzu.

Get in Touch

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Related Articles

YADDA ZA AYI RIJISTAR KWAS DA MAKARANTA DUNIYAR COMPUTER

https://www.youtube.com/watch?v=Livf5rpTkms Barka da zuwa Makarantar Duniyar Computer inda zaka iya yin kowane irin kwas kana zaune a...

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Get in Touch

20,224FansLike
2,252FollowersFollow
8,322SubscribersSubscribe

Latest Posts

YADDA ZA AYI RIJISTAR KWAS DA MAKARANTA DUNIYAR COMPUTER

https://www.youtube.com/watch?v=Livf5rpTkms Barka da zuwa Makarantar Duniyar Computer inda zaka iya yin kowane irin kwas kana zaune a...

Sharhin Littafin “Kwamfuta” Na Malam Salisu Hassan (Webmaster)

Sharhin Abdullahi Salihu Abubakar (Baban Sadik) daga jaridar Aminiya https://aminiya.dailytrust.com.ng/sharhin-littafin-kwamfuta-na-malam-salisu-hassan-webmaster-1/ A ranar Asabar, 28 ga watan Disamba 2019...

HANYOYIN DA AKE BI A CUCI MUTANE A INTANET

Wannan ita ce tattaunawa da muka yi a gidan Radio FM na Freedom da ake samun shi a lamba 29.9 FM a...

Yadda ake gane Facebook accout da aka yi hacking da yadda a magance shi

Ba abin mamaki bane ka bude shafinka na facebook ka wayi gari ka ga wani mara mutunci ya kwace ragamar tafiyar da shafin naka....

Shin wani zai iya amfani da BVN ya satar min kudi a Banki na?

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yawan yi a lokacin da kamfanoni ko ma’aikatu suka nemi mutum ya bayar da lambobin...