Ramadan Web Design

  4
  1800

  Wannan darasi ne da muka gabatar a watan Ramadan domin dalibai wadanda suke son su koyi yadda ake kirkiran shafi na Intanet.

  A wannan kwas mutum zai iya sanin dukkan wadansu surkulle da ake yin amfani da su domin kirkrian shafukan Intanet.

  Duk da karatun anyi shi ne a cikin aji tare da dalibai, amma Malamin yayi kokari wurin ganin ya yi bayanai masu gamsarwa game da hanyoyi da kuma ilimi da mutum zai yi amfani da su domin sanin yadda ake kirkirar shafuka a Intanet.

  Kasancewar darasi ne a kwanaki 12 kuma an tattara kusan fannoni da dama da ake bukatar saninsu wurin gina shafuka a Intanet tun daga abin da ya shafi darasi a matakin farko na sanin hanyoyin HTML da CSS da amfani da Notepad wurin gina shafi, haka amyi amfani da Abode Dreamweaver domin karasa karatun.

  Haka zalika, an koyar da yadda ake amfani da manhaja ta WordPress domin sanin yadda gidajen jaridu da mujallu suke amfani da wannan tsarin wurin kirkirar shafukan da suke yada labarai.

  Za ayi hakuri da surutu da tambayoyin dalibai kasancewar darussan dukansu anyi su a gadan dalibai kuma ambasu damar suyi tambayoyi kamar yadda aka sani a alada ta makaranta.

   

  4 SHARHI

  1. Comment:SLM alaikum dnyar computer inamuku fatan alkairi inasan nashiga class4 amma daga class 3 taqi haurawa Dan Allah yazanyi nagode

  2. Assalamu alaikun Duniyar Computer.
   Allah kara muku hazaka.
   Wallahi bisa karatun mu na WEB DESIGN ina kokarin shiga darasi na 11 sai muka sami matsala na network a wajen my, Wanda hakan yasa ban Iya karasa sauran darusan ba.
   Yanzu kuma na dawo sai abin yaki kuma.
   Toh Allahu alam. Ya zanyi yanzu?
   Daga Dalibin Ku na waje Mustapha Usman.
   Salem.

  3. Assalamu alaikum. Godiya Mara adadi bisa wannan darasi na Web designed Allah kara Basira Amin.
   Daga karshe shawarina shine yakamata ace akwai git link akarkashin kowane darasi musanman Wanda akayi da note ++ ta yadda zai kara saukaka ma dalibai.

  BAR AMSA

  Yi sharhin ka
  Shigar da suna a nan