An kirkiri manhajar waya ta tiyatar ido

Masana ilimin kimiyya a Birtaniya sun kirkiro wata manhajar wayar komai da ruwanka, da za ta kawo gagarumin sauyi a bangaren kula da idanu a kasashe masu tasowa.

Manhajar za ta baiwa ma’aikatan lafiya damar duba wa ko akwai cuta a ido, kuma su yi gwaji da na’ura ‘yar karama mafi araha.

a matsalar ido a kasashe masu tasowa na yankunan karkara, inda likitocin idanun da za su taimaka musu ba sa iya zuwa.

Mutane fiye da miliyan 285 ne a fadin duniya, ke fama da matsalar gani ko kuma makanta.

Ana tunanin cewa za a iya rigakafi ko magance hudu zuwa biyar na matsalolin ido, ta hanyar yin tiyatar yanar ido mai sauki, ko kuma ma amfani da tabarau.

A yanzu haka ana kan gwajin wannan manhaja a kan mutane 5000 a wasu kauyuka na kasar Kenya.

Daga BBC HAUSA

SHARE
Previous articleGoogle zai soma fassara zuwa Hausa
Next articleRAYUWAR MATASANMU A DANDALIN FACEBOOK (1)
Shugaban kamfanin Duniyar Computer, kuma Babban Editan Mujallar Duniyar Computer, mutum ne mai son sanar da mutane abin da Allah ya sanar da shi game da fannoni masu yawa. Mai kokari ne a fannin ilimin, Computer, Web Design, Android Development

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here