AKWAI VIRUS A WAYAR KA KA SANI KUWA?

1
628

Virus Na Waya (Phones)

Virus na wayar-tafi-da-gidanka kamar virus na computer ne, abin da ake nufi da virus shi ne wani file ne da yake yin aiki musamman domin ya bata ko lalata wani bangare na computer mutum ko kuma wayarsa. Kodayake computer virus yana yaduwa ne a sanadiyar email da kuma downloading daga internet, shi ma virus na waya yana yaduwa ne ta downloading daga internet ko kuma ta karbar sakon MMS (Multimedia Messaging Service) ko kuma ta turo sako daga bluetooth. Sau tari a wannan lokaci virus da suke shiga wayoyin hannu suna shiga ne ta wajen turo maka wani abu daga computer. Kodayake virus da yake shiga daga wata waya zuwa wata har yanzu bai gama shahara ba.

Virus na waya da zai iya shiga ta wata waya yafi yawane ga masu amfani wayar da take amfani da tsari na Symbian, kodayake wadanda suke rubuta shi wannan virus na waya ba su wani samu karbuwa ba a duniyar kamfanonin da suke yin waya ballantana su sami wani karfi, dalilin haka ya kasance ko da anyi wani virus na waya za ka samu bai cika bata wayar ba gaba daya.

Yaya aka yi suka yadu?

Duk wanda yake amfani da wayar da kawai sai dai a kira shi ko kuma ya amsa waya ko kuma ya kira ya aika da sakon SMS ya kwantar da hankalin shi babu wani virus da zai sami wayar shi.

Amma dukkanin wata waya da take da Bluetooth sannan kuma za ka iya karbar sakon MMS ko kuma ka yi browsing da wayarka za ta iya kamuwa da virus na waya. Waya tana da virus da dama wadanda suke iya yaduwa ta hanyoyi guda uku

  • Downloading a Internet – virus na waya yana yaduwa ta internet kamar yadda aka sani virus na computer yake yaduwa. Mutum zai shiga internet da wayar shi ya ga wani file ko game ko kuma hoto ko kuma theme ya yi mashi ya saukar da shi zuwa wayarshi ashe yana tattare da virus bai sani ba.
  • Karbar sako ta Bluetooth – virus na waya yana iya yaduwa a sakamakon Bluetooth din wayarka da ka bude domin wani ya aiko maka da sako, sai aka yi rashin sa’a ita wayar tashi akwai virus a ciki to duk sakon da ya aiko maka da shi zai taho tare da virus.
  • Multimedia Messaging Service (MMS) – wannan wani dama ce da wayar ka take baka idan kana son ka aika da sokon hoto ko kuma sakon video ga wani abokin ka ko kuma wata waya ba tare da Bluetooth ba ko kuma internet, kamfanin da kake amfani da layinsu su suke da alhakin baka wannan dama ko da wayar  tana supporting MMS, wanda shi virus da ya shigo a sakamakon MMS yafi hadari saboda zai shiga cikin contacts dinka ne kai tsaye ya rinka aika wa sauran mutanenka wannan virus din.

Kada ka manta dukkanin wani virus na waya ko na computer mataki daya suke bi shi ne dole sai ka yi installing dinsu a cikin wayar ko kuma computer za su iya yin aiki, da wannan dalili ne ya kasance mafi wayan virus sun fi zuwa tare da games ko kuma wani program da za a ce idan ka sakashi zai iya tsare ka daga wani abu.

Commwarrior Virus an samu bullowar shi a Janairun 2005 kuma shi ne virus na farko da ya fara shiga wayar tafi da gidan ka har ya iya yin ta’adi, kuma wani abin mamaki zai iya watsa kan shi a dan kankanin lokaci ga kusan duk mutumin da ke da waya kuma yabar wayar a bude kusa da wanda yake da wannan virus din. Yadda yake yada kan shi shi ne ta hanya ta Bluetooth da MMS, da zarar ka sami sakon wannan virus sannan kuma ka yi installing dinshi, kai tsaye zai fara neman wata wayar da Bluetooth dinta yake a kunne, da zarar ya samu zai aika da wannan virus ga wannan wayar. Haka shi wannan virus na Commwarrior zai kuma shiga cikin contact list dinka ya tura masu sakon MMS da shi wannan virus. (ya kake ganin idan ka ga sako daga webmaster za ka karba ko za ka ki karba?). Shi ya sa commwarrior virus ya zama shahararren virus da ya damu mutane a wancan lokacin tun da yana amfani da hanyoyi biyu ne wajen yada kan shi.

Saboda haka ya virus din yake yi idan har ya shiga wayar ka?

Barnar da yake yi.

Virus na waya na farko da aka sani shi ne Cabir duk da yake ba ya wani cutarwa ko kada, abin da kawai yake yi shi ne zai shiga wayarka ne kawai ya yi ta kokarin yada kan shi. Kodayake daman mafi yawan virus na waya ba su cika cutarwa ba. sosai

Kadan daga cikin abin da virus na waya ke iya yi shi ne ya shiga ya share dukkan wani contact da kake da su, ko kuma ya goge wata Kalandar da ka shirya a wayarka da makamantan haka, sannan kuma zai iya kwashe sunayen mutanen da suke cikin yawar ka gaba daya ya dauki wani hoto a cikin wannan wayar taka ta dauka virus a cikin shi ya kuma aika wa kowa da yake cikin contacts naka. Wani abin haushi da irin wannan MMS virus shi ne baya da watsa kan shi da yake yi, haka kuma yana yin amfani da kudin da kake da shi a waya tun da shi MMS ba kamar SMS ba ne, ana cire kudi da dan dama. Abu kuma mafi muni shi ne zai iya neman wani application da ke cikin wayarka ya lalata shi, ko kuma ya lalata wayar gaba dayan ta ta zamanto bata da amfani.

Ga wasu daga cikin virus na waya guda biyar da bayani game da su.

Sunan Virus: Cabir.A

·               Lokaci da ka fara jin labarin shi: June 2004

·               Wayar da yake kai wa hari: Symbian Series 60 phone

·               Hanyar da yake yada kan shi: updating

·               Irin cutarwar da yake yi: Baya cutar wa

·               Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/cabir.shtml

Sunan Virus: Skulls.A

·               Lokaci da ka fara jin labarin shi: November 2004

·               Wayar da yake kai wa hari: Symbian phones

·               Hanyar da yake yada kan shi: Downloading a Internet

·               Irin cutarwar da yake yi: yana hana ka komai a wayar illa kira da amsa kira

·               Karin bayani: http://www.f-secure.com/v-descs/skulls.shtml

Sunan Virus: Commwarrior.A

·               Lokaci da ka fara jin labarin shi: January 2005

·               Wayar da yake kai wa hari: Symbian Series 60 phones

·               Hanyar da yake yada kan shi: Bluetooth da MMS

·               Irin cutarwar da yake yi: yana aika wa da sako MMS ga duk wanda yake cikin contact

·               Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/commwarrior.shtml

Sunan Virus: Locknut.B

·               Lokaci da ka fara jin labarin shi: March 2005

·               Wayar da yake kai wa hari: Symbian Series 60 phones

·               Hanyar da yake yada kan shi: Downloading ta Internet

·               Irin cutarwar da yake yi: yana lalata system ROM, sannan ya hana dukkan wani abu aiki a cikin ita wayar, sannan ya sake saka maka wani malware acikin wayar ka

·               Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/locknut_b.shtml

Sunan Virus: Fontal.A

·               Lokaci da ka fara jin labarin shi: April 2005

·               Wayar da yake kai wa hari: Symbian Series 60 phones

·               Hanyar da yake yada kan shi: Downloading ta Internet

·               Irin cutarwar da yake yi: yana hana ta tashi, idan kuma an samu ta tashin sannan ya hana dukkan wani abu aiki a cikin ita wayar, sannan ya sake saka maka wani malware a cikin wayar ka

·               Karin bayani: ): http://www.f-secure.com/v-descs/fontal_a.shtml

Yadda za ka tsare wayar ka

Babbar hanyar da za ka iya tare wayar ka daga kamuwa da wani virus tayi daidai da hanyar da ake tsare computer daga kamuwa da virus, wannan ba wata hanya bace illa kada ka bude wani abu ba ka san daga inda yake ba ko kuma baka da garantin waye ya aiko maka da shi

  • Matakin farko ka kashe Bluetooth, ka saka ta a ‘hidden’ wato kada kowa ya ganta.
  • Mataki na biyu shi ne ko da wani lokaci ka rinka shiga kamfanin da suka yi wayar ka kana dubawa idan sun yi wani sabon program (update) na wayar ka ka saka domin da yin haka ne suke toshe dukkan wata kafa da masu rubuta virus suka samu suke cutarwar.
  • Mataki na uku Kayi installing wani anti-virus ko kuma wani program da zai tsare maka ita wayar taka daga shigowar virus

Daga karshe nake kira ga dukkan wanda ya san yana amfani da waya musamman wayar da take da dan tsada ya rinka yin software update na wayar domin muhimmancinsa, da fatar wannan rubutu zai anfanar.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here