Abubuwa Bakwai Da Bai Kamata Yara Na Yi Ba A Internet

Ba sabon abu ba ne idan kana da na’ura mai aiki da lantarki kamar kwamfuta, wayar salula nau’in (Android da Iphone) da ke da ƙarfin internet ka ga cewar yaron ka na neman ya fika iya amfani da su. Saboda yawan gogayya da yanayin zamani.
A saboda haka ne ya zama dole iyaye su yi taka tsantsan ga abubuwan da yaransu ke yi a shafukan inaternet kai har ma da kallace-kallacen satelite da talabijin.
Bayan ɓata tarbiya yaran da internet zai iya kawowa, yakan iya sa su gamu da yin mu’amala da azzalumai kuma batattun mutane.
Abubuwan da za a kiyaye guda bakwai su ne:

1 – Magana da baƙin da ba su sani ba:

Yin hulɗa ko magana da waɗanda ba su sani ba a internet ko social media. Da yawa akan ruɗi yara ta wannan hanyar a kuma jefa su cikin wani mugun hali na rayuwa.

2 –  Faɗan sirri su:

Babba ya san abin da ya daci ya watsa a cikinn internet amma yaro bai san haka ba. Dole a dinga kwaɓarsu da kuma lura da irin bayanan da suke watsawa duniya.

3 – Ɓata lokutan su ba iyaka

Mafi yawancin yara zak samu suna sauko (download) da ko guga game ba tare da yin la’akari da lokutan su ba. Wannan kan iya cutar da su wajen koma baya ga karatunsu, mu’amala da dai sauran su.

4 – Saukar da kaya (Apps) da bai dace ba

Google Play da Apple Store na da dubunnan apps da akayi domin ƙara kyautata rayuwar mu. Amma ya kamata a san irin Apps da yara kan saukar kan wayarsu da kuma irin bayanan da ake saka ma su. Da yawa daga cikin irin waɗannan Apps su na da haɗari sosai musamman ma ga yara. Yara su dinga tambayar manyansu kafin su saukar ko fara amfani da kowanne irin Manhaja (Apps).

5 – Shi ga shafin da bai dace ba ga yara

Da gangan yara kan iya shiga shafin da bai kamace su ba su ga abubuwan da ba su da kyau kamar na tsiraici. Ya kamata iyaye nan ma su lura da duba tarihin shafukan da yaransu ke buɗewa a intanet (browse history) domin ganin abubuwan da suke yi.

6 – Tsammanin cin kyauta:

A lokaci-lokaci mukan samu saƙwannin cewar mun ci wata gaggarumar kyauta ta gasa saboda haka domin karɓar wannan kyautar za ka aika da wasu bayanan ka na sirri. Saboda haka iyaye su lura su kuma tarbiyantar da yara game da irin wannan harkokin domin su kiyaye. Su san cewan ba wanda haka siddan zai ɗauki gagarumin kyauta ko kuɗi ya ba su kawai dan sun aika mashi da bayanan sirrin su.

7 Musgunwar Azzalumai:

Wasu kan musguna wa yara ta shafin internet da kuma yi masu baraza ga rayuwar su cewar idan suka sake suka faɗa wa wani abin da ke tsakanin su. Iyaye su dinga duba ko lura da yanayin ‘ya’yansu a lokacin da suke amfani da shafin internet idan sun ga canji su sa masu alamar tambaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here